Sauki Ya Zo: An Samu Hanyar da Za a Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Najeriya

Sauki Ya Zo: An Samu Hanyar da Za a Kawo Karshen 'Yan Bindiga a Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya za ta samu sauƙi a yaƙin da take yi da ƴan ta’adda da ke dagula zaman lafiya a tsakanin al'umma
  • Hakan ya faru ne saboda wani matashi ɗan Najeriya da ke zaune a Burtaniya ya ƙirƙiro wata manhajar AI wacce za ta taimaka wajen gano ƴan bindiga
  • Yunusa Jibrin ya bayyana cewa idan har gwamnati ta amince da sakamakon binciken nasa, zai taimaka matuƙa wajen samun nasarar yaƙi da ta'addanci a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani ɗan Najeriya mazaunin ƙasar Burtaniya, Yunusa Jibrin, ya ce ya ƙirƙiro wata manhajar 'Artificial Intelligence' (AI) don gano ƴan bindiga da maɓoyarsu a Najeriya.

Jibrin ya bayyana cewa binciken nasa idan gwamnatin tarayya ta amince da shi, zai taimaka wajen ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen gano tare da kawar da ƴan bindiga a duk inda suke a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hotuna sun bayyana yayin da aka gudanar da salloli na musamman a Zaria

Yunusa Jibrin ya kirkiro sabuwar manhaja
Binciken Yunusa Jibrin ka iya kawo karshen 'yan bindiga Hoto: Yunusa Jibrin
Asali: Facebook

Matashin wanda ya kammala karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar kwamfuta daga jami’ar Sussex, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Vanguard a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya yi amfani da fasahar haɗa hotuna ta ƙirƙirarriyar fasahar AI domin samar da dubunnan hotunan da ke nuna ƴan bindiga a cikin hamada.

Jibrin ya ba da cikakken bayani game da bincikensa

A kalamansa:

"Na ɗauki sabuwar hanya, ta yin amfani da haɗin gwiwar hoto na AI don samar da dubunnan hotunan da ke nuna ƴan bindiga a cikin hamada, ɗauke da makamai da motoci.
"Bayan samun waɗannan bayanai, na yi amfani da samfurin 'Vision Transformer' domin gane ƴan ta'adda a cikin hotunan, inda aka samu daidaito mai kyau a yayin gwajin farko.

Da yake bayar da goyon bayansa, masanin kwamfutar daga jihar Gombe wanda ya jagoranci tawagar masu bincike daga kwalejin ilmi ta tarayya ta Fatiskum, ya jaddada bukatar yaƙi da ƴan ta’adda ta hanyar fasaha ta zamani.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya jero jihohin Arewa 3 da ya kamata sojoji su tashi tsaye kan ƴan Bindiga

Ya kuma bayyana cewa zai haɗa gwiwa da gwamnatin tarayya wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro da ke kawo koma baya ga ci gaban ƙasar nan.

Sojoji Sun Ragargaji Ƴan Ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi ruwan wuta kan ƴan ta'addan da suka addabi al'ummar jihar Zamfara.

Sojojin a yayin musayar wutan da suka yi da ƴan ta'addan sun sheƙe da.dama daga cikinsu tare da ceto mutanen da suka sace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel