Zamfara: Jami’an Tsaro Sun Yi Nasarar Cafke Dan Ta’addam da Ya Addabi Jama’a, Ya Yi Bayani

Zamfara: Jami’an Tsaro Sun Yi Nasarar Cafke Dan Ta’addam da Ya Addabi Jama’a, Ya Yi Bayani

  • Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun yi nasarar cafke wani kasurgumin dan ta’adda da ya addabi al’ummar jihar da hare-hare
  • Wanda aka cafken mai suna, Dan Umaru Abubakar kamar yadda ya tabbatar a faifan bidiyo ya kai hare-hare da dama
  • Kasurgumin dan bindigan da ya shiga hannu, Dan Umaru ya na daga cikin wadanda suka sace daliban Jami’ar Gusau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Jami’an tsaro a jihar Zamfara sun yi nasarar kama daya daga cikin kasurgumin 'yan bindiga da suka addabi jihar.

Kasurgumin dan bindigan da ya shiga hannu mai suna Dan Umaru Abubakar yana daga cikin wadanda suka sace dalibai mata a Jami’ar Gusau.

Kara karanta wannan

'Dan gida ya fasa kwai, ya jefi Gwamnatin Tinubu da biyewa manufofin turawa

An cafke kasurgumin dan ta'adda da ya addabi al'ummar jihar Arewa
Dan Umaru na daga cikin 'yan bindigan da suka sace dalibai a Gusau. Hoto: Nigerian Police Force, @ZagazolaMakama.
Asali: Facebook

Yadda 'yan bindiga suka sace daliban Jami'a

Idan ba a manta ba a bara ‘yan bindiga sun sace dalibai mata da ke Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zagazola Makama ta wallafa wani faifan bidiyo inda dan bidigan ke bayani lokacin da ake yi masa tambayoyi kan harin.

Dan Umaru wanda ya ce ya fito daga garin Kuraji ya lissafo wasu manyan ‘yan ta’adda da suka hada baki domin sace daliban.

Ya ce akwai dabar Mallam Tukur da ta Dogo Gide inda ya ce shi ya na daga cikin dabar Mallam Tukur wanda suka zo su biyar.

Ya lissafo 'yan bindigan da suka kai harin tare

Ya lissafo wadanda suka fito daga dabar Malam Tukur inda ya ce su biyar suka zo da suka hada da Dan Goggo da Shehu da Manga da Babuga da wani yaro.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara zafi a APC yayin da dakarun ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriya a jihar Arewa

Dan Umaru ya kara da cewa ‘yan dabar Dogo Gide akalla sun zo da yara sun fi mutum 100 wadanda suka yi hadaka domin sace daliban.

Har ila yau, Dan Umaru ya ce sun kuma sace Jan Bako sai da shi bai fito harin ba, tawagar Mallam Tukur ne suka sace shi.

Wannan na zuwa ne yayin da hare-haren ‘yan bindiga ya yi kamari a Arewa maso Yamma musamman a yankunan karkara.

Yan bindiga sun sace dalibai a Zamfara

A baya, kun ji cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da sace wasu dalibai biyu da ke Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an sace daliban ne da ke dakin kwanansu a kusa da Jami’ar a unguwar Sabon Garin Damba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel