'Yan Bindiga Sun Shiga Har Cikin Masallaci Sun Sace Masallata a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Shiga Har Cikin Masallaci Sun Sace Masallata a Jihar Arewa

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai sabon hari a garin Tsafe hedikwatar ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai sun yi awon gaba da masallata masu tarin yawa yayin da suke shirin fara sallar Asuba
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun yi basaja ne bayan sun aje baburansu a wajen gari don kada a gano su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu masallata a ɗaya daga cikin masallatan garin Tsafe hedikwatar ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin mai suna Garba ya shaidawa jaridar The Punch cewa ƴan bindigan sun mamaye masallacin ne da misalin ƙarfe 5:00 na safiyar ranar Alhamis a lokacin da mutanen ke shirin fara sallar Asuba.

Kara karanta wannan

Dandutse: Ƴan bindiga sun kashe babban soja da wasu jami'ai biyu, sun tafka ɓarna kan bayin Allah

'Yan bindiga sun sace masallata a Zamfara
'Yan bindiga sun yi awon gaba da masallata a Zamfara Hoto: @daudalawal
Asali: Twitter

Yadda lamarin ya auku

Garba ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yau alhamis za mu fara sallar Asuba, kwatsam sai ga su (ƴan bindiga) suka shigo masallaci suka umarci kowa ya fita ya bi su.
"Kowa ya nemi hanyar tsira amma ƴan bindigan sun tare ko’ina tare da gargaɗin cewa za su kashe duk wanda ya yi yunƙurin guduwa.
"Na samu na yi tsalle daga taga inda da sauri na shiga ɗaya daga cikin gine-ginen da ba a kammala ba kusa da masallacin inda na ɓoye kaina."

Garba ya ci gaba da cewa ƴan bindigan sun bar baburansu nesa da masallacin don kada masu ibada su lura da motsinsu.

A cewar Garba, adadin masallatan da aka sace zai iya wuce 30.

Ya ƙara da cewa masallacin ya cika da mutane lokacin da ƴan bindigan suka kai harin kuma kaɗan ne daga cikin mutanen suka tsira.

Kara karanta wannan

Yan sanda da sojoji sun yi kazamin artabu da ƴan bindiga, sun samu nasara a jihar Arewa

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Ɗaya daga cikin shugabannin al’ummar da ya zanta da jaridar ta wayar tarho da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jami’an rundunar Askarawan Zamfara, na ci gaba da bin sawun ƴan bindigan domin kuɓutar da mutanen da suka sace.

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, kan lamarin, inda ya bayyana cewa zuwansa ofis kenan, amma zai kira domin bada ƙarin bayani.

Sai dai, bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Faɗa Ya Ɓarƙe Tsakanin Ƴan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu ɓarkewar rikicin a tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindigan da ke a jihar Zamfara.

Faɗan wanda ya ɓarke ya jawo sanadiyyar halaka manyan shugabannin ƴan bindiga guda biyar a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel