"Obi Ya Ci Amana Ta," Sabon Mai Magana da Yawun Atiku Ya Tada Hazo Ana Shirin Zabe
- Kenneth Okonkwo ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da ƙwarewarsa duk da cewa ya taɓa sukar sa a bainar jama'a
- Tsohon kakakin Peter Obi ya zargi tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na LP da cin amanarsa, yana mai cewa rashin yanke hukunci ya sa bai dace ya jagoranci Najeriya ba
- Okonkwo ya ce Atiku ya fi mayar da hankali kan abin da mutum zai iya bayarwa wajen gina ƙasa, ba wai kalaman suka da aka taɓa yi masa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja – Fitaccen ɗan wasan Nollywood da ya koma siyasa, Kenneth Okonkwo, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya gane ƙimarsa duk da cewa ya taɓa sukar sa a baya.
Okonkwo ya kuma zargi tsohon ubangidansa a siyasa, Peter Obi, da cin amanarsa, yana mai cewa shi ne ya karya amana tsakaninsu.

Source: Instagram
"Obi bai dace da shugaban Najeriya ba"
Tsohon kakakin Peter Obi a jam'iyyar Labour Party ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV ranar Alhamis.
Jawabin nasa ya zo ne kwana ɗaya bayan an naɗa shi kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaɓen 2027.
Okonkwo ya ce tun a shekarar 2024 ya sanar da jama'a cewa ya daina aiki tare da Obi, bayan ya fahimci cewa tsohon gwamnan Anambra ba shi da jajircewar da ake buƙata domin jagorantar Najeriya.
"Na ga wasu halaye a tare da shi da suka nuna bai dace ya zama shugaban ƙasar Najeriya ba. Na faɗi hakan a fili ne domin mutane su san cewa ba na masa magana a lokacin."
'Peter Obi ne ya ci amanata'
Okonkwo ya ce bayan ya kammala aikinsa tare da Obi, ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a matsayin mai sharhi kan harkokin siyasa.
Sai dai ya dage cewa Peter Obi ne ya karya amana tsakaninsu.
"Shi ne ya ci amanata," in ji Okonkwo.
Tsohon ɗan wasan ya ce duk da cewa ya fi sukar Atiku Abubakar fiye da Peter Obi a baya, tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai bari hakan ya hana shi ganin ƙimarsa ba.
A cewarsa, Atiku ya yi watsi da kiraye-kirayen wasu da suka tuna masa irin sukar da ya taɓa yi masa, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne irin gudummawar da mutum zai iya bayarwa wajen gina Najeriya.
Ya yabawa Atiku kan gano hazakarsa
Okonkwo ya bayyana Atiku a matsayin jagoran da ke da baiwar gano hazaka, yana mai cewa ya taimaka wajen bai wa fitattun mutane damar yin hidima ga ƙasa.
Ya ambaci sunayen Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, Farfesa Charles Soludo da Nasir El-Rufai a matsayin wasu daga cikin mutanen da Atiku ya ba dama a baya.
A cewarsa, abin da Atiku ke dubawa shi ne ƙimar da mutum zai ƙara wa ƙasa, ba kalaman suka da aka taɓa yi masa ba.
Asali: Legit.ng

