'Hukuncin da Kotu Ta Yanke kan Rikicin Jam'iyyar ADC Ya Wanke Tinubu daga Zargi'
- Karaminin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ce hukuncin kotu kan shugabancin ADC ya tabbatar Tinubu ba ya tsoma baki a harkokin shari'a
- Ministan ya ce hukuncin ya tabbatar da Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar ADC na kasa
- Matawalle ya kuma zargi wasu yan adawa da yada karya da farfaganda domin ba ta sunan Shugaba Bola Tinubu a wurin yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan shugabancin ADC ya wanke Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga zargin tsoma baki a harkokin bangaren shari'a.
Matawalle ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Juma'a, 3 ga watan Yulin 2026 a Kaduna.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Kotu ta ƙwace Naira miliyan 150 na wani 'dan Majalisar tarayya a Najeriya

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kotun ta yi watsi da karar da ke kalubalantar shugabancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark a ADC.
Ta kuma yanke hukuncin cewa tsarin da aka bi wajen nada shugaban ADC na kasa da sauran shugabanni ya yi daidai da kundin tsarin mulkin jam'iyyar da kuma doka.
Matawalle ya yi martani kan hukuncin
Da yake tsokaci kan hakan, Matawalle ya ce yadda Shugaba Tinubu bai tsoma baki a hukuncin ba ya nuna irin jajircewarsa wajen kare dimokuradiyya da 'yancin bangaren shari'a.
Ya ce hukuncin ya tabbatar da sahihancin shugabancin David Mark, tare da karyata zarge-zargen da ke cewa Tinubu na katsalandan a bangaren shari'a ko kuma yana kokarin kafa tsarin jam'iyya daya a Najeriya.
"Shugaba Tinubu ya mutunta doka"
Ministan ya ce hukuncin kotun ya sake nuna cewa Shugaba Tinubu na mutunta bin doka, ka'idojin shari'a da kuma 'yancin bangaren shari'a.
Ya kara da cewa shugaban kasa bai taba tsoma baki cikin shari'o'in siyasa masu sarkakiya ba, duk da suka da zarge-zargen da wasu 'yan adawa ke yi masa.
A cewarsa, tarihin Tinubu wajen fafutukar dawo da dimokuradiyya tun kafin ya zama shugaban kasa ya tabbatar da irin kishinsa ga tsarin dimokuradiyya.
Ya ce shugaban ya fahimci muhimmancin kare cibiyoyin dimokuradiyya, yana kallon bangaren shari'a mai zaman kansa a matsayin ginshikin zaman lafiya, hadin kan kasa da dorewar dimokuradiyya.

Source: Twitter
Ya zargi 'yan adawa da yada farfaganda
Matawalle ya zargi wasu 'yan siyasar adawa da yada karya da farfaganda domin bata sunan Shugaba Tinubu duk lokacin da hukuncin kotu bai zo daidai da bukatunsu ba.
Ya ce irin wadannan mutane ba sa yabawa bangaren shari'a idan hukuncin ya nuna babu katsalandan daga bangaren gwamnati, cewar rahoton Punch.
Don haka ya bukaci 'yan Najeriya su rika duba hukuncin kotu cikin adalci tare da yaba wa shugaban kasa bisa kokarinsa na karfafa cibiyoyin dimokuradiyya.
Matawalle ya hangi nasarar Tinubu
A baya, kun ji cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya bayyana kwarin gwiwa cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kuri’un 'yan Arewa a 2027.
Matawale ya nuna tabbacin cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu ƙarin goyon bayan Arewa a zaɓen 2027 saboda ingantattun tsare-tsaren tsaro da ya kawo.
Ministan ya jaddada cewa babu wata farfaganda, yaɗa ƙarya ko suka daga ‘yan adawa da za su iya karkatar da hankalin Shugaban ƙasa daga aiwatar da aikinsa yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng
