Boko Haram: Sama da 90% Na Ainihin Masu Aƙidar Ta'addanci Sun Mutu Inji Zulum

Boko Haram: Sama da 90% Na Ainihin Masu Aƙidar Ta'addanci Sun Mutu Inji Zulum

  • Gwamnatin Borno ƙarƙashin Farfesa Babagana Zulum, ta ce kashi 95 cikin 100 na masu tsattsaurar akidar Boko Haram sun mutu ko sun tuba
  • Mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro, Ishaq Abdullahi, ya faɗi yadda mafi yawan waɗanda suka kafa kungiyar suka mutu
  • A cewarsa, yaƙin da ya ɓarke tsakanin ISWAP da mayaƙan Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Sheƙau a 2021 ya taimaka matuƙa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta ce sama da kashi 95 na mutanen da ke da akidar Boko Haram, musamman wadanda suka kafa ta ko dai sun mutu ko kuma sun mika wuya.

Mai bada shawara ta musamman ga gwamnan jihar Borno kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Ishaq Abdullahi mai ritaya ne ya faɗi haka yayin hira da Daily Trust a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano ya ba 'yan kasuwa muhimmiyar shawara kan azumin watan Ramadan

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum.
Kaso 95 Cikin 100 Na Masu Akidar Boko Haram Sun Baƙunci Lahira, Gwamnatin Borno Hoto: Prof. Babagana Umaru Zulum
Asali: Facebook

Yayin wannan hira ranar Lahadi, ya ce shugabancin kungiyar mai hatsari na cikin yanayi domin kusan mutum 10 ne kawai daga cikin wadanda suka kafa ta ne a raye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ya manyan ƴan Boko Haram suka mutu?

Abdullahi ya bayyana cewa mafi akasarin manyan kwamandojojin ƙungiyar sun baƙunci lahira a yaƙin da ya ɓarke tsakanin ISWAP da mayaƙan Boko Haram.

A cewarsa, da yawan ƴan ta'adda sun mutu a faɗan cikin gida kan shugabanci tsakanin mambobin ISWAP da suka ɓalle da mayakan da ke goyon bayan Abubakar Shekau bayan ya mutu a 2021.

"Daya daga cikin shugabanninsu ya ce cikin mutum 300 da suka fara ƙafa kungiyar Boko Haram tun 2009, kasa da 10 ne kaɗai suka rage a raye a yanzu.
"Hatta sauran mutum 10 da suka rage sun watse saboda rikicin mulki. Wasu sun mutu sakamakon cizon macizai a daji, wasu sun mutu sakamakon luguden sojoji."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hotuna sun bayyana yayin da aka gudanar da salloli na musamman a Zaria

"Wasu kuma ruwan damina ya cinye su, wasu kuma raunin harbin bindiga ya zama ajalinsu yayin da wasu suka bi sahun waɗanda suka mika wuya cikin shekaru biyu da suka wuce.

- Ishaq Abdullahi

Mutuwar Sheƙau ta ci Boko Haram

Ya kuma ƙara da cewa wasu daga cikin masu aƙidar Boko Haram sun baƙunci lahira ne sakamakon yaƙin cikin gida musamman bayan mutuwar Sheƙau.

Abdullahi ya ce mutuwar Sheƙau ta yi sanadin kashe sama da kaso 90 na masu riƙaƙƙiyar aƙidar Boko Haram, rahoton Vanguard.

Wane irin nasarori sojoji ke samu a Arewa?

A wani rahoton kuma Sojojin Najeriya da wasu jami'an tsaro sun kashe ƴan bindiga 13 tare da kama mutane 271 da ake zargi a jihohi 3 na Arewa.

Mataimakin kwamandan rundunar Operation Safe Haven, Terzungwe Iyua, ne ya bayyana haka a hedkwatar ƴan sanda da ke Jos ranar Jumu'a

Asali: Legit.ng

Online view pixel