Darika da Izala: Bayan Sallah, an Dakatar da Sauran Ibada a Masallatan Jami'ar ATBU

Darika da Izala: Bayan Sallah, an Dakatar da Sauran Ibada a Masallatan Jami'ar ATBU

  • Jami'ar ATBU da ke jihar Bauchi ta yi karin bayani game da matakan da ta dauka game gudanar da ayyukan addini a faɗin makarantar
  • Mai magana da yawun jami'ar, Malam Zailani Bappah ya bayyana cewa za a takaita ayyukan ibada da salloli biyar da sallar Juma'a kadai a halin yanzu
  • Hakan ya biyo bayan sabanin da aka samu a makarantar game da ba 'yan Darikar Tijjaniyya fili su gina masallacin da za su rika amfani da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi ta sanar da dakatar da dukkan ayyukan addini da ake gudanarwa bayan sallolin farilla biyar da kuma sallar Juma'a.

Sanarwar da jami'ar ta fitar ta nuna cewa za a cigaba da zama a haka har sai kwamitin da aka kafa ya kammala nazari tare da gabatar da shawarwarinsa kan ƙudurorin da aka cimma a wani taro da jami'an DSS.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu bayan kai hari a Katsina

Bakin shiga jami'ar ATBU
Kofar jami'ar ATBU da ke Bauchi. Hoto: Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi
Source: UGC

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da matakin da jami'ar ta dauka ne a wani bidiyon hira da mai magana da yawun ATBU da Albarka Radio ya wallafa a Facebook.

Bayanin shugaban jami'ar ATBU

Shugaban jami'ar ATBU, Farfesa Ibrahim Hassan Garba, ya tabbatar da cewa an dakatar da dukkan wasu ayyuka a masallacin makarantar sai salloli biyar da Juma'a.

Ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da wani kwamitin mutum 13 da ya ƙunshi wakilai daga shugabancin jami'ar da sauran kungiyoyin ɗalibai.

Wadanda suka halarci zaman sun hada da kwamitin shura, ƙungiyar TIMSAN, MSSN, kungiyar al'umar Kiristocin jami'ar ATBU da sauran masu ruwa da tsaki.

Aikin da kwamitin ATBU zai yi

Rahotanni sun nuna cewa an ɗaura wa kwamitin alhakin tsara dokoki da ƙa'idojin da za su jagoranci gudanar da harkokin addini a cikin jami'ar.

Bugu da kari, Legit Hausa ta gano cewa ana sa ran kwamitin da aka kafa zai kammala aikinsa tare da miƙa rahotonsa cikin makonni biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari cibiyar NIPSS, an gwabza fada da jami'an tsaro

Limamin masallacin jami'ar ATBU
Sheikh Mansur Isa Yelwa da ke limanci a jami'ar ATBU. Hoto: Professor Mansur Isa Yelwa
Source: Facebook

Bayanin kakakin jami'ar ATBU

Kakakin jami'ar ATBU, Malam Zainali Bappah ya bayyana cewa an cimma wasu muhimman abubuwan a zaman da aka yi da DSS.

Daga cikin abubuwan da aka tattauna a kansu, ya tabbatar da cewa an bukaci makarantar ta dawo lura da masallatai da kanta, ciki har da nada limamai.

Ya bukaci a rika ba dukkan 'yan makaranta dama su samu wakilici a kungiyoyin ɗalibai kuma kowane bangare ya samu shiga kwamitin shura.

Daga cikin abubuwan da zamana ya cimma akwai soke ba dalibai 'yan Tijjaniyya fili domin su gina masallacin da suka kebanta da shi.

A karshe, ya bukaci dukkan dokokin jami'ar su yi aiki kan harkokin addini, inda a yanzu kwamitin da aka kafa zai mika rahoto a mako biyu masu zuwa.

Farfesa Yelwa ya dawo limanci

A wani labarin, mun kawo muku cewa Farfesa Mansur Isa Yelwa ya sanar da cewa ya dawo limanci a jami'ar ATBU da ke jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: An daura sunan Atiku cikin 'yan takara a shafin INEC

Ya sanar da haka ne kwanaki kadan bayan ya ce zai bar jagorancin masallacin matukar jami'ar ba ta soke hukuncin gina wani masallaci da za a yi ba.

A bayanin da ya yi, malamin ya sanar da cewa ya yi zama da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki na jami'ar kafin yanke matakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng