Ministan Tinubu Ya Jero Jihohin Arewa 3 da Ya Kamata Sojoji Su Tashi Tsaye Kan Ƴan Bindiga

Ministan Tinubu Ya Jero Jihohin Arewa 3 da Ya Kamata Sojoji Su Tashi Tsaye Kan Ƴan Bindiga

  • Bello Matawalle ya buƙaci dakarun sojin Najeriya su kara zage dantse a yaƙin da suke da ƴan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma
  • Karamin ministan tsaron ya ce ya kamata sojoji su tashi tsaye kan matsalar tsaro musamman a jihohin Katsina, Kaduna da Zamfara
  • Ya kuma roƙi ɗaukacin al'umma su ci gaba da bai wa jami'an tsaro goyon baya yayin da suke kokarin tsare lafiyarsu da dukiyoyinsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya buƙaci rundunar soji ta ƙara matsa ƙaimi a yaƙin da take da ƴan ta'adda da ƴan bindiga a Arewa maso Yamma.

Matawalle ya ce yawaitar hare-haren ƴan bindiga a jihohin musamman a Kaduna, Katsina da Zamfara ya ƙara nuna buƙatar ƙara girke jami'an soji a yankin.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya yun yi luguden wuta kan ƴan ta'adda, sun tura da dama lahira

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.
Matawalle Ya Bukaci a Kara Yawan Ayyukan Sojoji a Katsina, Kaduna da Zamfara Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

Wane jihohi ne Matawalle ya hango matsala?

Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce tabarɓarewa tsaron ta kai ga ƴan ta'adda da ƴan bindiga na kai hari kan jami'an tsaro, ana asarar rayuka da dama a shiyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma jaddada bukatar hadin kai tsakanin hukumomin tsaro don samun damar kawar da ta'addanci da sauran nau'ukan laifuka a yankin, rahotonmu.

Ya ce:

"Tsaro da kwanciyar hankalin ƴan ƙasa shi ne abu mafi muhimmanci kuma ya zama wajibi a ɗauki tsauraran matakai domin magance ayyukan ƴan ta'adda da ƴan bindiga."

- Bello Matawalle

Matawalle ya yi magana kan manoma

Ministan ya bayyana cewa magance dukkan ayyukan ta'addanci ba samar da tsaro kaɗai zai yi ba, hakan zai ba jama'a kyakkyawan yanayin da zasu ci gaba da noma.

"Samar da tsaro a yankin ba kawai zai kare rayuka da dukiyoyin al'umma kaɗai bane, har ma da inganta ayyukan noma. Manoma zasu samu damar shuka har su girbe amfanin gona ba tare da tsoron hari ba.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Asirin wasu ƴan bindiga 15 ya tonu, sun fara sakin bayanai a jihar Arewa

"Kuma wannan zai kara tabbatar da wadatar abinci da kuma haɓakar tattalin arziki a yankin na Arewa maso Yamma."

- Bello Matawalle.

Matawalle ya bukaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro goyon baya a kokarinsu na kawar da miyagu a yankin, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

Zanga-zanga ta ɓalle kan rashin tsaro a Katsina

A wani rahoton kuma Fusatattun mazauna kauyen Wurma a karamar hukumar Kurfi sun tsohe babban titin Katsina-Dutsinma kan hare-haren ƴan bindiga.

Masu zanga-zangar sun hana matafiya wucewa, lamarin da ya tilasta wa ababen hawa canza hanya domin tafiya garuruwan da suka nufa a sassan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel