Sojoji Sun Sheke Shugaban Ƴan Bindiga da Tawagarsa Ta Addabi Jihar Katsina

Sojoji Sun Sheke Shugaban Ƴan Bindiga da Tawagarsa Ta Addabi Jihar Katsina

  • Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe Maikusa, daya daga cikin manyan shugabannin 'yan ta'adda a jihar Katsine
  • Kakakin rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya sanar da hakan, inda ya ce sojoji sun yi artabu da 'yan bindigar a ranar Litinin
  • Wannan ya biyo bayan wani samame da dakarun sojojin ke kai wa a dazuzzukan kananan hukumomin Kurfi da Safana da ke jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - Rundunar sojojin Najeriya a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin kasar ta bayyana cewa dakarunta sun kashe wani kasurgumin 'dan ta'adda mai suna Maikusa.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa Maikusa shi ne na biyu a jerin shugabannin ‘yan bindiga da ke barna a yankin Katsina, karkashin jagorancin dan ta’adda Modi Modi.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojojin Najeriya yun yi luguden wuta kan ƴan ta'adda, sun tura da dama lahira

Sojoji sun kashe Maikusa, rikakken dan bindiga a Katsina.
Sojoji sun kashe Maikusa, rikakken dan bindiga a Katsina. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Samamen sojoji ya zama silar kashe Maikusa

AIT Live ta ruwaito cewa sojoji sun bindige Maikusa da wasu ‘yan ta’adda guda uku ne a wata musayar wuta da suka yi a ranar Litinin 4 ga Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakarun sun kai samame kan ‘yan ta’addan ne a kananan hukumomin Kurfi da Safana na jihar, kamar yadda kakakin rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya sanar.

Rundunar ta bayyana cewa kai harin ya taimaka wajen nasarar fatattakar ‘yan ta’adda daga yankunan.

Sojoji sun matsa wa 'yan bindiga a Katsina

Sanarwar ta kara da cewa, a yayin farmakin, sojojin sun fuskanci turjiya daga 'yan bindigar amma sun yi galaba a kan su.

Bayan artabun ne sojojin suka kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, gidan harsashai uku, harsashai 65 na musamman kirar 7.62mm, bindigar baushe da kakin sojoji.

Kara karanta wannan

An karrama sojoji 8 da suka ƙi karbar cin hancin naira miliyan 1.5 daga hannun ɓarayin shanu

Sojojin sun kuma lalata sansanonin ‘yan ta’adda a kauyukan Wurma, Shaiskawa, Yauni, da Dogon Marke a karamar hukumar Kurfi, da kuma kauyukan Ummadau da Zakka da ke karamar hukumar Safana, duk a jihar Katsina.

Katsina: Yan bindiga sun kashe babban soja

A wani labarin da Legit Hausa ta ruwaito, 'yan bindiga sun kashe wani kaftin din soja da wasu jami'an soji guda uku a garin Sabo da ke shiyyar Funtua.

Sanata mai wakiltar mazabar shiyyar Funtua (daga jihar Katsina), Muntari Dandutse ya bayyana hakan a gaban zauren majalisar dattawa a ranar 21 ga watan Fabrairu,.

Asali: Legit.ng

Online view pixel