Dubu Ta Cika: Sojoji Sun Cafke Jami'an Tsaro da Ke Safarar Makamai ga 'Yan Ta'adda

Dubu Ta Cika: Sojoji Sun Cafke Jami'an Tsaro da Ke Safarar Makamai ga 'Yan Ta'adda

  • Dubun wasu jami'an tsaro na hukumomin NSDC da NCos da ke safarar makamai ga miyagu ta cika bayan sun fada komar dakarun sojoji
  • Dakarun sojoji na rundunar Operation Udoka sun cafke jami'an tsaron ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu
  • Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar cafke wani mutum da ake zargin mamba ne na kungiyar 'yan ta'adda ta IPOB/ESN

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Enugu - Dakarun hadin gwiwa na shiyyar Kudu maso Gabas na rundunae Operation Udoka sun dakile wata hanyar samar da makamai ba bisa ka'ida ba.

Sojojin sun cafke jami'an hukumar NSCDC guda biyu da jami'in hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa NCoS guda daya, saboda zarginsu da sayar da makamai ga bata-gari a shiyyar Kudu maso Gabas.

Sojoji sun kama jami'an tsaro
Dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin kasa ta Najeriya ta fitar a shafinta na X, ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu bayan kai hari a Katsina

Sojoji sun kama jami'an tsaro

Dakarun sun kama mataimakin sufuritanda II Obaji Sampson na hukumar NSCDC, Sufuritanda Tasie Victor Nnamdi, mai kula da ma'ajiyar makamai na rundunar NSCDC ta jihar Enugu, da kuma Ekwueme Onyebuchi Clement.

Sanarwar ta ce kamun na zuwa ne a matsayin ci gaba da kai hare-hare kan bata-gari a fadin shiyyar Kudu maso Gabas, lamarin da ya haifar da nasarori ta hanyar ayyukan da suka dogara da bayanan sirri da kuma hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

An kama masu safarar makamai

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Ayyukan sun kai ga kama mutane da dama da ake zargi da hannu a aikata laifuffuka da kuma gano makamai, alburusai da sauran kayayyakin laifi, wanda hakan ke kara karfafa kokarin inganta tsaro a yankin."
“A wani farmakin na daban, samun bayanan sirri daga runduna ta 82 ya kai ga kama Obaji Sampson na hukumar NSCDC."
“Bincike ya kai ga kama sufuritanda Tasie Victor Nnamdi, mai kula da ma'ajiyar makamai na rundunar NSCDC ta jihar Enugu, wanda aka gano shi ne babban mai samar da makaman, da kuma Ekwueme Onyebuchi Clement, wanda aka gano shi ne babban mai karba."

Kara karanta wannan

Jirgin sojojin Najeriya ya far wa yan bindiga kimanin 200, ya musu gagarumar illa a Neja

“Kamun ya fallasa wata hanyar da ake zargi ta samar da makamai ba bisa ka'ida ba."
“Bayan samun karin bayanan sirri, dakarun rundunar Operation UDOKA, tare da hadin gwiwar 'yan sandan sojoji sun kai samame wani gida a Titin Achara, Trans-Ekulu, Golf Estate, a jihar Enugu, inda aka kama wani da ake zargi mamba ne na IPOB/ESN kuma mai safarar makamai, Friday Nnanna."
An cafke jami'an tsaro a Enugu
Daya daga cikin jami'an tsaron da aka cafke Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sama na Najeriya sun farmaki 'yan ta'adda da dama a jihar Niger.

Dakarun sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun kashe 'yan ta'adda da dama a hare-haren sama da suka kai a karamar hukumar Mariga.

An kaddamar da farmakin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa sama da 'yan ta'adda 200 dauke da babura suna tafiya ta hanyar Sangeko zuwa Dogon Dawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng