Abin da zai Hana Farashin Litar Fetur Sauka zuwa 'kasa da N1,000 a Najeriya
- Farashin fetur a Najeriya na iya ci gaba da kasancewa sama da N1,000 kan kowace lita duk da saukar farashin ɗanyen mai a duniya
- A yanzu haka, Matatar Dangote ta ce masu shigo da fetur daga ƙasashen waje su rage farashi maimakon jiran sai ta fara rage wa kamar yadda aka saba
- Matatar ta ce har yanzu tana da ɗanyen mai da aka saya da tsada, lamarin da ke hana rage farashin cikin gaggawa duk da saukan farashi a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Rahotanni sun gano cewa farashin fetur a Najeriya na iya ci gaba da kasancewa sama da Naira 1,000 kan kowace lita na wani lokaci.
Lamarin zai ci gaba da zama a haka har sai dai idan masu shigo da man fetur daga ƙasashen waje sun fara gasa ta rage farashi da Matatar Dangote.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa bayan saukar farashin ɗanyen mai zuwa kusan Dala 70 kan ganga sakamakon dawowar jigilar mai ta mashigar Hormuz, mutane da dama sun yi tsammanin farashin fetur zai koma kamar da.
An yi magana kan matatar mai
Wani babban jami'in rukunin kamfanonin Dangote, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda muhimmancin batun, ya ce gwamnati ta fi dacewa ta nemi masu lasisin shigo da fetur su rage farashinsu.
Jami'in ya ce ya yi mamakin yadda masu shigo da fetur daga Rasha, wanda ya ce ya fi araha, ba su rage farashin sayarwa ba da gangan.
Ya ce:
"Gwamnatin Tarayya ta ba da lasisin shigo da fetur da yawa a watannin nan. Idan suna shigo da fetur mai araha daga Rasha, me ya sa ba sa sayar da shi da rahusa?"
Lokacin da aka gaya masa cewa watakila masu shigo da fetur suna jiran Matatar Dangote ta fara rage farashi, sai ya ce:
"Ta yaya za su ce suna jiranmu, alhali jiragensu na ci gaba da iso kullum?"
Dalilin rashin saukar farashin fetur
Jami'in ya bayyana cewa matatar har yanzu tana da ɗimbin ɗanyen mai da aka saya lokacin da farashinsa yake da tsada, wanda ya sa ba zai yiwu a rage farashin fetur cikin gaggawa ba.
Ya ce kamfanin na da manyan tankunan adana ɗanyen mai, sannan akwai wasu jiragen ruwa da ke kan hanya zuwa Najeriya tare da ɗanyen mai, yayin da aka riga aka kulla yarjejeniyar sayen wasu ƙarin kaya.

Source: Original
A ganawarsa da majiyar Legit, Sakataren kudi na IPMAN reshen Jihar Kano, Musa Yahya Mai Kifi, bayyana cewa suna sayen man fetur da tsada bai dace a tilasta masu su sayar da sauki ba.
A kalamansa:
"Idan an saida mana mai da sauki, mu ma za mu sayar da sauki, shi ne kawai matsayarmu. Kuma yanzu duk lokacin da da farashin ya ragu mu ma muna rage wa"
"In kin duba sati biyu da ya rage man kamar a nan Kano ya kai N1,385 kusan a lokacin ba haka ake saida wa ba? To amma ga shi yanzu ya gangaro har ya dawo N1,270 a mafi gidajen mai."
Za a samu saukin fetur a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa ana sa ran za a samu sauki a gidajen mai bayan matatar Dangote ta rage farashin da take sayar da man fetur ga 'yan kasuwa a Najeriya, inda ake sa ran za su yi wa jama'a ragi.
Matatar Dangote ta rage farashin da take sayar da litar man fetur ga 'yan kasuwa 'yan kwanaki bayan ta dauki irin wannan mataki a lokacin da yanayin farashi ke ci gaba da sauya wa a kasuwar duniya.
Sabon farashin na ragin Naira 50 kan kowace lita, shi ne karo na biyu da aka samu ragi a cikin kwanaki bakwai kacal, inda a baya aka rage daga Naira 1,175 zuwa Naira 1,125 kan kowace lita.
Asali: Legit.ng


