Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

  • Dakarun sojoji na Operation Hadarin Daji sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'addan da suka addabi jihar Zamfara
  • Dakarun sojojin sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda masu yawa a wani harin kwanton ɓauna da suka kai musu
  • A yayin kwanton ɓaunan da sojojin suka yiwa ƴan ta'addan, sun kuma samu nasarar ceto wasu mutum takwas da aka yi garkuwa da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) dake shiyyar Arewa maso Yamma sun kashe ƴan bindiga da dama tare da lalata matsugunansu a jihar Zamfara.

Dakarun sojojin sun kuma kuɓutar da wasu mutum takwas da aka yi garkuwa da su a yankin Bayan Ruwa na jihar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun dira kan ƴan bindiga, sun kashe su da yawa sun ceto mutum 40 a Arewa

Sojoji sun halaka 'yan ta'adda a Zamfara
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Zamfara Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Operation Hadarin Daji, Laftanar Suleiman Omale ya fitar a ranar Laraba a Gusau ya bayyana cewa dakarun sun sake samun nasarar fatattakar ƴan ta’addan a ci gaba da aikin kakkaɓe ƴan ta'adda a jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"A nasarar da aka samu a baya-bayan nan, sojojin sun ceto mutum takwas da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba a wani harin kwanton ɓauna da suka kai a jihar.

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda

Ya bayyana cewa, a yayin farmakin sojojin sun yi wa ƴan ta’addan ruwan wuta, wanda saboda tsananin azaba ya sanya suka gudu suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.

A kalamansa:

"Don haka martanin da sojojin suka kai a kan lokaci da gaggawa ya kai ga ceto mutum takwas da aka yi garkuwa da su ba tare da sun jikkata ba."

Kara karanta wannan

Yan sanda da sojoji sun yi kazamin artabu da ƴan bindiga, sun samu nasara a jihar Arewa

A cewarsa, sojojin da suka yi nasarar kakkabe ƴan ta’adda da dama sun lalata maɓoyar ƴan ta’addan tare da mamaye yankin wajen yin sintirin nuna ƙarfin iko a yankin.

Ya bayyana cewa dukkan waɗanda aka ceto an miƙa su ga hukumomin da suka dace domin haɗa su da iyalansu.

An Karrama Sojoji 8 a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu sojojin Najeriya sun nuna tsantar gaskiya da kishin aikinsu a jihar Plateau.

Sojojin waɗanda suka ƙi karɓar karɓar cin hancin miliyan 1.5 sun samu karramawa ta musamman, domin yaba wa da ƙwazon da suka nuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel