An Yi Kazamin Karo Tsakanin Kungiyoyin ‘Yan Bindiga 2 a Jihar Arewa, Da Dama Sun Mutu

An Yi Kazamin Karo Tsakanin Kungiyoyin ‘Yan Bindiga 2 a Jihar Arewa, Da Dama Sun Mutu

  • Mummunan karo ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga guda biyu a tsakanin Gusau da karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara
  • An fara barin wuta mai zafi tsakanin mayakan Kachallah Mai Yankuzu da na Dogo Balli tun da karfe 7:00 na safiyar Lahadi
  • Fadan ya fara ne bayan mayakan Dogo Balli sun kai wa na Yankuzu harin bazata a mabuyarsu, kuma an rasa rayuka daga bangarorin biyu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Zamfara - Rahotanni sun kawo cewa mayakan ta'addanci da dama sun mutu yayin wani kazamin karo tsakanin kungiyoyin adawa na 'yan bindiga guda biyu.

Lamarin ya afku ne a tsakanin Mada kan hanyar Gusau da karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Murja Kunya na shirin daukar mataki 1 tak kan gwamnatin Kano

An yi karo tsakanin 'yan bindiga a Zamfara
An Yi Kazamin Karo Tsakanin Kungiyoyin ‘Yan Bindiga 2 a Jihar Arewa, Da Dama Sun Mutu Hoto: HumAngle
Asali: UGC

Zagazola Makama ya rahoto cewa kazamin karon ya afku ne a safiyar ranar Lahadi, 25 ga watan Fabrairu, tsakanin manyan kungiyoyin 'yan bindiga guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda fada ya kaure tsakanin mayakan Yankuzu da Balli

Ya ce karon da aka yi tsakanin mabiyan Kachallah Mai Yankuzu da Dogo Balli, yana daya daga cikin karo mafi muni da aka yi tsakanin kungiyoyin hamayyar guda biyu.

An tattaro cewa Dogo Balli ya tara mayakansa domin su kai harin bazata mabuyar Yankuzu, wanda ya yi sanadiyar yin musayar wuta mai zafi tun daga karfe 7:00 na safe.

Majiyoyin sun bayyana cewa an kashe mayaka masu yawan gaske daga bangarorin biyu, yayin da fadan ke kara zafi har zuwa lokacin kawo wannan rahoton.

Ku tuna cewa ’yan ta’addan sun yi ta kashe-kashe da kuma yin garkuwa da su a Gusau da karamar hukumar Tsafe.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mutuwar mutum hannun jami'an tsaro ya sa an nemi Gwamna ya tashi tsaye

Har ila yau, su ne ke da alhakin yin garkuwa da mutane a Danmusa da Kankara.

An tsige kakakin majalisar Zamfara saboda rashin tsaro

A wani labarin, mun ji a baya cewa majalisar jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, sannan ta maye gurbinsa da Bashar Gummi.

Tsige Moriki da majalisar ta yi ya biyo bayan kudirin da 'dan majalisa mai wakiltar mazabar Maru, Nasiru Abdullahi ya gabatar

Mambobin majalisar 18 daga cikin 24 sun amince da kudirin na neman tsige kakakin yayin wani taron gaggawa da suka gudanar a daren Alhamis, 22 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel