Dan a Mutun Tinubu Ya Ƙare Oluremi, Ya ba da Labarin Attajira Mai Sayar da Ƙosai a Abuja
- DeWani masoyin Bola Tinubu ya yaba wa Sanata Oluremi Tinubu kan shirinta na ƙarfafa mata a Najeriya
- Ya yi amfani da labarin Asabe mai sayar da kosai da koko a Abuja, wadda ta gina gidaje daga ribar kasuwancinta
- Matashin wanda dan a mutun APC ne ya buƙaci gwamnati da masu ruwa da tsaki su tallafa wa mata da jari, horo da kasuwanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wani fitaccen mai goyon bayan Bola Ahmed Tinubu, Khamis Musa Darazo, ya yaba wa matarsa kan tallafawa mata.
Darazo ya yaba wa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, bisa ƙoƙarinta na ƙarfafa mata bayan kalamanta kan tallar kosai.

Source: Facebook
Darazo ya bayyana haka ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook inda ya ziyarci Asabe mai koko da kosai a Abuja.
Tallar kosai: Dan APC ya goyi bayan Oluremi
Ya bayyana wa wakilin Legit Hausa cewa shirye-shiryen da take aiwatarwa na taimakawa wajen bunƙasa tattalin arziƙi, ƙarfafa zaman lafiyar iyalai da kuma inganta ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Ya ce nasarar mata da dama a Najeriya ba ta dogara da samun manyan jarin kasuwanci kaɗai ba, illa jajircewa, ladabi da samun damar bunƙasa sana'arsu.
Yayin da yake magana kan tasirin kasuwancin ƙananan sana'o'i, Darazo ya kawo misalin Asabe, wata 'yar kasuwa da ke Abuja, domin nuna ƙarfin matan Najeriya.
Ya ce Asabe ta gina gidaje ne daga ribar sayar da akara da koko, lamarin da ya nuna cewa babu halalacciyar sana'ar da ta yi ƙanƙanta wajen samar da arziki.
Ya ce:
"Na san wata jajirtacciyar mace mai suna Asabe a Abuja wadda ta gina gidaje daga ribar da ta samu wajen sayar da ƙosai da koko.
"Labarinta tunatarwa ne cewa babu wata halattacciyar sana'a da ba za ta iya samar da arziki ba.
Da jajircewa, kyakkyawan tsarin tafiyar da kuɗi, ƙananan sana'o'i na iya samar da manyan nasarori."
Darazo ya ce wannan ne ya sa ajandar Sanata Oluremi Tinubu ta ƙarfafa mata take da muhimmanci, domin idan mata sun samu ƙarfi, iyalai da al'umma sukan bunƙasa.

Source: Facebook
Shawarar Darazo ga gwamnatoci, kamfanoni
Darazo ya buƙaci gwamnatoci, cibiyoyin kuɗi, kamfanoni masu zaman kansu da abokan hulɗar ci gaba su haɗa kai wajen tallafa wa mata da jari mai sauƙi.
Haka kuma ya buƙaci a samar wa mata horon sana'a, jagoranci a harkokin kasuwanci da kuma inganta hanyoyin samun kasuwanni domin bunƙasa sana'o'insu.
Ya kuma ƙarfafa matasan Najeriya su rungumi sana'o'i, yana mai cewa akwai mutunci a kowace halattacciyar sana'a, tare da sake jaddada goyon bayansa ga Ajandar 'Renewed Hope' ta Bola Tinubu.
Kwastam: Dan APC ya ba Tinubu shawara
A wani labarin, kun ji cewa wani mai goyon bayan Shugaba Tinubu, Khamis Musa Darazo, ya ba da muhimman shawarwari gamea da hukumar Kwastam.
Darazo ya ce ritayar manyan jami'ai lokaci guda na iya haifar da giɓin shugabanci da kawo cikas ga gyare-gyare da tara kuɗaɗen shiga.
Ya kirayi ga Tinubu da ya tabbatar da ƙarin wa'adi domin tabbatar da ci gaba da kuma shirya sababbin shugabanni cikin tsari.
Asali: Legit.ng

