Sojoji Sun Yi Gumurzu da 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno, an Rasa Rayuka

Sojoji Sun Yi Gumurzu da 'Yan Ta'addan ISWAP a Borno, an Rasa Rayuka

  • 'Yan ta'addan ISWAP dauke da makamai sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke karamar hukumar Guzamala a jihar Borno
  • Dakarun sojoji sun samu nasarar dakile harin bayan sun yi artabu da hatsabiban 'yan ta'addan na ISWAP a tsakar dare
  • Gumurzun da aka yi tsakanin bangarorin biyu, ya jawo an samu asarar rayuka a tsakanin sojoji da 'yan ta'addan ISWAP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - 'Yan ta'addan ISWAP sun kashe sojoji biyu da wani mamba guda daya na kungiyar CJTF a jihar Borno.

Sojojin sun rasa rayukansu yayin da suke fatattakar wani harin tsakar dare da ƙungiyar ISWAP ta kai a Mairari, da ke karamar hukumar Guzamala a jihar Borno.

Sojoji sun gwabza fada da 'yan ta'addan ISWAP
Dakarun sojojin Najeriya a cikin daji Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Mukaddashin jami'in yaɗa labarai rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabas ta "Operation Hadin Kai", Kyaftin Muhammed Goni, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 2 ga watan Yulin 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun ji jiki da dakarun sojoji suka farmake su a Plateau

Sojoji sun fatattaki 'yan ISWAP

A cewarsa, dakarun CIB XIX, yayin da suke fatattakar harin da aka kai wa wani sansanin sojoji a yankin a ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2026 sun yi wa 'yan ta'addan barna mai yawa.

"Rundunar haɗin gwiwa ta (Arewa maso Gabas), Operation Hadin Kai (OPHK), ta sake nuna juriya da fifikon yaƙi yayin da dakarun CIB XIX a sansanin sojoji da ke Mairari suka yi nasarar fatattakar wani gagarumin harin dare da 'yan ta'addan ISWAP suka kai a Mairari, da ke karamar hukumar Guzamala a jihar Borno."
“A ranar 1 ga Yuli, 2026, da misalin ƙarfe 1:25 na dare, 'yan ta'addan sun ƙaddamar da hari a sansanin. Dakarun sun mayar da martani da jajircewa ta musamman, inda suka shiga gumurzu da maharan a cikin wani kazamin musayar wuta."
"Wanda hakan ya tilasta musu ja da baya cikin rudani bayan sun yi wa 'yan ta'addan barna mai yawa tare da lalata kayayyakinsu.”

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Sojoji sun cafke jami'an tsaro da ke safarar makamai ga 'yan ta'adda

- Kyaftin Muhammed Goni

Kayayyakin da aka kwato a hannun 'yan ta'adda

Ya lissafta abubuwan da aka ƙwato wadanda suka haɗa da bindigogin AK-47, albarusai da harsasai, da abin harba makami mai linzami na RPG da sauran su.

Ya ƙara da cewa faifan bidiyo na sa ido ya tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun kwashe gawarwaki da da dama da wadanda aka raunata yayin artabun.

“Za a iya tunawa cewa al'ummar Mairari a kwanan nan ne aka sake tsugunar da su, inda iyalai sama da 950 suka koma yankin."

- Kyaftin Muhammed Goni

Sojoji sun fafata da 'yan ta'addan ISWAP
Dakarun sojojin Najeriya a bakin daga Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

An rasa ran sojoji

Harin, a cewarsa, wani yunƙuri ne na fidda rai da 'yan ta'addan suka yi na dasa tsoro a tsakanin mazauna yankin da kuma kawo cikas ga tsarin sake tsugunar da mutane da ake ci gaba da yi.

“Sai dai, an dakile manufarsu, domin ba a samu asarar rayukan farar hula ko ɗaya ba a cikin al'ummar yankin lokacin da aka kai harin."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu bayan kai hari a Katsina

“Abin baƙin ciki shi ne, sojoji biyu da mamba ɗaya na CJTF sun sadaukar da rayuwarsu a lokacin wancan gumurzu mai zafi."

- Kyaftin Muhammed Goni

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Enduring Peace sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda a jihar Plateau.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka akalla mutane shida da ake zargiin 'yan ta'adda ne bayan an yi musayar wuta.

Sojojin sun kuma samu nasarar kwato bindigogin da aka ƙera a cikin gida a jerin samamen da suka kai a faɗin jihar Plateau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng