'Yan Ta'adda Sun Bindige Yaro Dan Shekara 10, Sun Sace Matan Aure a Sokoto

'Yan Ta'adda Sun Bindige Yaro Dan Shekara 10, Sun Sace Matan Aure a Sokoto

  • 'Yan bindiga sun kashe wani yaro dan shekara 10 tare da sace akalla mutum 43 a hare-hare a ƙauyukan Takatsaba da Tarah aSokoto
  • An bayyana cewa daga cikin waɗanda aka sace akwai matan aure, yara da matar limamin ƙauye, kuma an jikkata wasu a harin
  • Mazauna wuraren da abin ya shafa sun koka kan rashin samun agajin jami'an tsaro, tare da cewa 'yan ta'addan na makamai masu hadari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Akalla mutum 43 ne ake zargin 'yan bindiga sun sace a hare-hare da suka kai a ƙauyukan Takatsaba da Tarah da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

Majiyoyi daga yankin sun ce maharan ɗauke da manyan makamai sun kai farmaki ƙauyukan ne a daren Laraba, inda suka riƙa harbe-harbe kafin su bi gidaje suna kwasar mutane.

Kara karanta wannan

Bayan shan wuta, mayakin ISWAP na kan kogi ya mika wuya ga jami'an sojoji

Taswirar jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Wani mazaunin ƙauyen Takatsaba, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda an sace wasu daga cikin danginsa, ya shaida wa Daily Trust cewa 'yan bindigar sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 11:30 na dare.

An harbe dan shekara 10

Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'adda sun kashe ɗan shekara 10 daga gidan Abdullahi Ado, sannan suka sace mutum 32 daga gidaje bakwai a Takatsaba da Tarah.

Ya ce daga cikin waɗanda aka sace akwai mutum tara daga gidan Mamman Dogo; mutum biyar daga gidan Abdullahi Ado, inda aka kashe ɗansa mai shekara 10; matar Babban Limamin ƙauyen.

Ya kara da cewa na sace mutum biyu daga gidan Mai Unguwa; yara marayu biyu daga gidan marigayi Malam Sani; mutum takwas daga gidan Malam Abubakar; da kuma mutum biyar daga gidan Amadu Siro.

Majiyar ta ƙara da cewa har yanzu ba a tantance inda wasu mazauna ƙauyen suke ba, domin da dama sun tsere zuwa daji yayin harin.

Kara karanta wannan

Yadda aka zargi dan Amurka da ba Iran bayanan sirrin Isra'ila domin ruguza ta

Ba a samu daukin hukuma ba

Leadership ta wallafa cewa wanda ya yi magana da manema labara ya kara da cewa jami'an tsaro ba su samu damar kawo ɗauki a lokacin harin ba.

"Jami'an tsaro suna iya ƙoƙarinsu, amma a wannan karon 'yan bindigar sun fi su dabara. Jami'an suna gefen yammacin ƙauyen, yayin da maharan suka shigo ta Kudu maso Gabas, suka aiwatar da harin sannan suka tsere,"

In ji shi.

Ya tuna cewa kwanaki takwas da suka gabata ma an kai hari ƙauyen, amma jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile shi.

Ya bayyana sunayen biyar daga cikin waɗanda aka sace a gidan Abdullahi Ado da suka haɗa da Abubakar, Basira, Amira, Aisha da Naja'atu, yana mai cewa dukkaninsu suna tsakanin shekaru 6 zuwa 16.

Gwamna Ahmed Aliyu
Gwamnan Sokoto na bayani a wajen taro. Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Source: Facebook

A ƙauyen Tarah, wani mazaunin yankin wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun isa ƙauyen da misalin ƙarfe 11:30 na dare, inda suka shafe kusan minti 50 suna kai hari.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan ta'adda suka hallaka 'yan Najeriya kusan 80,000 daga 2020 zuwa 2025

A cewarsa, maharan sun sace mutum 20, amma daga baya suka saki tara daga cikinsu bayan sun isa wani kogi inda suka kasa tafiya da dukkansu.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce zai binciki lamarin. Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, bai yi ƙarin bayani ba.

An kama makamai a Kebbi

A wani rahoton, mun kawo muku cewa dakarun sojin Najeriya sun kai farmaki wani gida da ake kera makamai a wani yanki na jihar Kebbi.

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an yi nasarar kama makamai da suka hada da bindigogi da sauransu a cikin gidan.

Sojoji sun kama mutum biyu daga cikin wadanda ake zargi da kera makamai da raba su ga 'yan ta'adda da ke kai hare-hare a jihohin Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng