Sanata Yari Ya Yi Magana Irin Ta Buhari Wanda Ya Kira Yan Najeriya Malalata
- Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa duk dan Najeriya da ba shi da kasala zai iya samun abinci a kan teburinsa
- Yari ya bayyana hakan ne yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC da aka gudanar a Uyo a Akwa Ibom
- Daraktan yakin neman zaben APC ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu, yana mai cewa ya kamata 'yan Najeriya su sake ba shi dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa duk dan Najeriya da ba shi da kasala zai iya samun abinci a kan teburinsa.
Sanata Yari ya yi maganan ne yayin da ake ci gaba da zagaya wa domin gudanar da yakin neman zaben Bola Tinubu kan zaben 2027.

Source: Twitter
Sanata Yari ya magantu kan yunwa a kasa
Yari ya bayyana hakan ne yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, cewar rahoton Vanguard.
Yayin jawabinsa, Yari ya amince cewa ana fama da yunwa a Najeriya, amma ya ce har yanzu ana samun kayan abinci a kasuwanni.
Sai dai ya yi tambaya mai kama zuciya da cewa ko akwai wani dan Akwa Ibom da ke da kudi a aljihunsa wanda ya je kasuwa amma ya rasa abincin da zai saya?
Sanata Yari ya ce idan babu abinci a kasuwa kuma yan kasa na da kudi wannan shi ake kira yunwa.
A kalamansa:
"Kamar yadda na fada, muna fama da yunwa. Bari in yi tambaya a nan. Mutanen Akwa Ibom, daga inda na fito, muna da abinci a kasuwa.
"Ban sani ba, a Akwa Ibom, akwai wanda ya kai kudinsa kasuwa ya gano babu shinkafa?
"Shin akwai wanda yake da kudi a aljihunsa, ya je kasuwa domin sayen kayan abinci amma ya tarar babu su?
"Idan babu abinci a kasuwa, wannan shi ne abin da muke kira yunwa. Amma duk wanda ba shi da kasala, tabbas zai samu abinci a kan teburinsa."

Source: Facebook
Yari ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu
Yayin da yake kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, Yari ya yi nuni da abin da ya bayyana a matsayin raguwar farashin kayan abinci.
Ya bukaci 'yan Najeriya su sake zabar Tinubu a karo na biyu, yana mai cewa nasarorin da gwamnatin ta samu za su zama ginshikin yakin neman zabensu.
Ya ce:
"Kamar yadda muka yi alkawari ga 'yan Najeriya, za mu gudanar da yakin neman zabe bisa alkalumanmu da abubuwan da muka yi wa 'yan Najeriya. Bisa haka ne muke neman su sake ba mu dama."
Sanata Yari ya ce Tinubu zai zarce
An ji cewa Abdulaziz Yari ya ce imanin Tinubu ga Allah, ayyukansa da kuma kokarin kwamitin yakin neman zaben APC za su taimaka masa wajen samun nasara a 2027.
Yari ya bayyana hakan ne a Makkah, Saudiyya, lokacin da ya raka Shugaba Tinubu da wasu manyan ‘yan Najeriya aikin Umrah.
Tsohon gwamnan Zamfara ya ce APC za ta yi amfani da ayyukan da ta gudanar wajen gamsar da ‘yan Najeriya su sake zaben Tinubu.
Asali: Legit.ng