Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani game da Hukuncin Kotu kan Atiku da ADC

Abubuwa 10 da Ya Kamata Ku Sani game da Hukuncin Kotu kan Atiku da ADC

Fagen siyasar Najeriya ya sake shiga wani yanayi na rudani bayan babbar kotun tarayya ta yanke hukunci ta hannun Mai Shari’a Peter Lifu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Hukuncin ya soke shugabancin jam’iyyar ADC karkashin David Mark, tare da rushe takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2027.

Abubuwan da ke cikin hukuncin kotu da ya rusa ADC
Atiku Abubakar da shugaban ADC, David Mark. Hoto: ADC Vanguard.
Source: Twitter

Kotu ta yi hukunci Atiku Abubakar na Kebbi

An yanke hukuncin ne yayin da dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ke gudanar da yakin neman zabe a jihar Kebbi.

Sai dai duk da haka Atiku ya ci gaba da neman al'umma yayin da ya fitar da sanarwa cewa babu gudu ba ja da baya kan takara a 2027.

Legit Hausa ta yi duba kan hukuncin da aka yanke game da shugabancin jam'iyyar ADC tafe da kawo muku wasu batutuwa game da shi

Kara karanta wannan

“Ko zai shafi Tinubu a 2027?” Yadda al’ummar Legas suka tarbi Kwankwaso ya ja hankali

Ga muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da hukuncin:

1. Muhimmin hukuncin kotu da wadanda abin ya shafa

Hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu ya soke shugabancin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark.

Baya ga tsige shugabancin jam’iyyar, kotun ta kuma soke zaben fidda gwani da aka gudanar a lokacin mulkinsu, cewar Punch.

Hakan ya rushe takarar Atiku Abubakar ta shugaban kasa a zaben 2027, tare da soke takarar sauran wadanda jam’iyyar ta tsayar a mukamai daban-daban.

2. Rikicin shugabancin Arewa maso Gabas

Yunkurin kalubalantar shugabancin ADC karkashin David Mark ya samo asali ne daga karar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, wadda Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa mai kula da shiyyar Arewa maso Gabas, ya shigar.

Nafiu ya kalubalanci sahihancin tsarin mika ragamar shugabancin jam’iyyar ga sabon shugabancin bayan murabus din tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Cif Ralph Nwosu.

Kotu ta yi fatali da shugabancin ADC
Shugaban jam'iyyar ADC, David Mark. Hoto: ADC Vanguard.
Source: Twitter

3. Kwace jam’iyyar da bangaren Atiku ya yi

Kara karanta wannan

Sama da kasa ba za su hade ba idan aka hana Atiku takara in ji ministan Tinubu

Rikicin ya samo asali ne bayan wani gagarumin sauyin sheka a siyasa, wanda ya kai ga kwararowar magoya bayan Atiku zuwa jam’iyyar ADC.

Masu sukar matakin da wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka nuna rashin amincewa da shi sun bayyana wannan shigowa a matsayin kwace jam’iyyar cikin gaggawa ba tare da bin ka’ida ba.

Sun yi zargin cewa manyan ƴan siyasa sun kwace tsarin tafiyar da jam’iyyar cikin dare daya, suka yi watsi da hanyoyin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

4. Rikicin neman iko da shugabancin jam’iyyar

Kwace ragamar jam’iyyar ya haifar da mummunan rikicin cikin gida kan wanda ya kamata ya jagoranci ADC da kuma yadda za a tafiyar da harkokinta.

Wasu bangarori da suka nuna rashin amincewa da sauyin shugabancin, ciki har da Nafiu Bala Gombe, sun yi zargin cewa nada Sanata David Mark, Ogbeni Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da tanade-tanaden dokar zabe.

Rikicin cikin gida ya rikide zuwa kazamin fada tsakanin bangarori kan wanda ke da halastaccen ikon tafiyar da jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ba ADC mafita kan rusa takarar Atiku da kotu ta yi

5. Kai karar zuwa Kotun Koli a Najeriya

Yayin da rikicin neman ikon tafiyar da jam’iyyar ke kara tsananta, bangarorin da ke takaddama sun garzaya kotu, lamarin da ya haifar da jerin umarnin wucin gadi, umarnin hana aiwatarwa da daukaka kara.

Takaddamar ta rika hawa matakai daban-daban na kotuna cikin gaggawa, har ta kai gaban Kotun Koli, inda bangarorin suka nemi samun halaccin iko na wucin gadi ko kuma hana abokan hamayyarsu gudanar da harkokin jam’iyyar.

Kotu ta rusa takarar Atiku
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Twitter

6. Umarnin mayar da shari’ar kotun farko

A wani mataki na shari’ar da ta dauki lokaci ana yi, kotunan daukaka kara sun yi nazari kan matakan shari’ar tare da bayar da umarnin mayar da bangarorin zuwa kotun da ta fara sauraron karar.

Maimakon yanke hukunci kan muhimman batutuwan shari’ar kai tsaye a matakin daukaka kara, manyan kotunan sun mayar da karar zuwa babbar kotun tarayya domin sauraro da yanke hukunci kan ainihin korafe-korafen da suka shafi hakkin shugabanci da bin ka’idojin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jita jita ta kare, INEC ta yi magana kan takarar Atiku bayan hukuncin kotu

7. Hukuncin da aka yanke da ya saba wa doka

Bayan bin matakan shari’ar, Mai Shari’a Lifu ya saurari ainihin karar tare da yanke hukunci a kan wanda ya shigar da ita.

Kotun ta bayyana cewa kafa kwamitin gudanarwa na kasa karkashin jagorancin David Mark ya saba wa kundin tsarin mulkin ADC da dokar zabe.

Saboda haka, dukkan matakai, taruka da zabukan fitar da gwani da aka gudanar karkashin wannan shugabanci ba su da ingancin doka, don haka kotun ta soke su.

8. Mataki na gaba: Daukaka kara zuwa gaba

Dambarwar shari’ar bai kare ba, wakilan ADC da bangarorin da hukuncin ya shafa sun bayyana aniyarsu ta kalubalantar hukuncin na jiya a Kotun Daukaka Kara.

Yayin da babban zaben 2027 ke kara karatowa, halaccin shugabancin jam’iyyar da takararta ta shugaban kasa na cikin wani mawuyacin hali, wanda ke nuna cewa za a sake samun wani babban saɓanin shari’a.

A karshe, bangaren Atiku ne ya taka muhimmiyar rawa wajen jefa ADC cikin halin da take ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotu: Adawa ta kara ƙarfi, jam'iyyun siyasa 9 sun goyi bayan ADC da Atiku

Jam'iyyu sun marawa ADC baya

An ji cewa kungiyar jam’iyyun adawa ta Coalition for Democracy ta yi Allah-wadai da hukuncin kotun da ya tsige shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark.

Jam’iyyun sun ce matakin na iya zama wani shiri na kawar da sahihan jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.

Sun yi kira ga sauran jam’iyyun adawa, ƙungiyoyin farar hula da ‘yan Najeriya su haɗa kai wajen kare dimokuraɗiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.