Atiku Ya Kaddamar da Kamfen a Sokoto, Ya Yi Muhimman Alkawura ga 'Yan Najeriya

Atiku Ya Kaddamar da Kamfen a Sokoto, Ya Yi Muhimman Alkawura ga 'Yan Najeriya

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin magance matsalar tsaro da dawo da zaman lafiya a Najeriya idan ya lashe zaɓen 2027
  • Atiku ya bayyana cewa zai dawo da fata ga matasa tare da samar da yanayin rayuwa mai sauƙi ga ’yan Najeriya
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya isa Sokoto domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro, dawo da fata ga ’yan Najeriya da kuma sauƙaƙa tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2016 bayan isarsa Jihar Sokoto domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan

ADC ta kawar da shakku, ta bayyana wurin kaddamar da kamfen din Atiku a Sokoto

Atiku ya je Sokoto kamfe
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taron ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nuna godiyarsa ga magoya bayan da suka tarbe shi a jihar. Ya bayyana Sokoto a matsayin muhimmiyar cibiyar tarihi da ta shahara wajen addini, ilimi da jagoranci.

Atiku ya ce ’yan Najeriya sun gaji da matsaloli

Atiku ya ce ’yan Najeriya sun gaji da yunwa, rashin tsaro da kuma alkawuran da ba a cika ba.

Ya bayyana cewa zaɓen 2027 wata dama ce da al’umma za su yi amfani da ita wajen kawo sauyi a shugabancin ƙasar.

A cikin saƙonsa, ya ce:

“’Yan Najeriya sun gaji da yunwa, tsoro da alkawuran da ba a cika ba. A yau, suna da zaɓi, tsari da kuma jagora da ke shirye ya kawo sauyi.”

Ya ƙara da cewa idan aka ba shi damar shugabantar ƙasar, zai magance matsalar tsaron da ke addabar al’ummomi, dawo da fata ga matasa tare da sauƙaƙa rayuwa ga jama’a.

Kara karanta wannan

Duk da zargin barazana, Atiku zai kaddamar da yakin neman zabensa a Sokoto

"Zan kawo ƙarshen rashin tsaron da ke addabar al’ummominmu, dawo da fata ga matasanmu, sannan in sa Najeriya ta zama ƙasa mai sauƙin rayuwa.” In ji shi.

Yaƙin neman zaɓen ADC ya fara daga Sokoto

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a Sokoto a matsayin farkon tafiyar da yaƙin neman ceton Najeriya.

Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa ADC za ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

“Tafiyar ceton Najeriya ta fara ne daga nan. Tare, za mu yi nasara.” In ji shi.

Kafin isowarsa, an ga dimbin magoya baya sun taru a wurare daban-daban a Sakkwato domin tarbarsa.

Batun zargin shirin kawo cikas ga ADC

Zuwan Atiku Sokoto ya zo ne kwana guda bayan ya yi zargin cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) na ɗaukar matakan kawo cikas ga yaƙin neman zaɓen ADC a jihar.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana damuwarsa kan lamarin kafin ya isa jihar domin gudanar da taron.

Sai dai DSS ta mayar da martani kan zargin, inda ta ce tana gudanar da bincike kan batun.

Kara karanta wannan

An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Jam’iyyar ADC na ci gaba da shirye-shiryen yaƙin neman zaɓenta gabanin babban zaɓen da ake sa ran gudanarwa a shekarar 2027.

Atiku ya je Sokoto
Atiku Abubakar na sauka daga jirgi don yakin neman zabe a Sokoto Hoto: @ADCVanguuard
Source: Twitter

ADC ta bayyana wurin kamfen a Sokoto

​A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta bayyana wurin da za ta gudanar da bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Sanata Ibrahim Lamido, mai kula da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar a Jihar Sokoto, ya bayyana cewa za a gudanar da taron ne a sakatariyar ADC da ke kan titin Ilorin, a cikin birnin Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng