Bakar Wahalar da ‘Yan ADC Suka Sha Wahala kafin Atiku Ya Shirya Kamfen a Sokoto
- Kashim Ibrahim Imam ya ce Gwamnan Jihar Sokoto ya hana su samun wurin gudanar da taron yakin zaben shugaban kasa
- Darektan yakin zaben ADC ya kuma yi zargin an hana su samun otal a Sokoto, inda aka umarci masu otal kada su ba mu ɗakuna
- Atiku Abubakar ya ce shugabannin ADC su je su sauka a gidajen abokansu kuma su fita su yi kamfe a kan titunan garin Sokoto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Sokoto - Kashim Ibrahim Imam ya bada labarin irin kalubalen da suka fuskanta kafin su shirya taron kamfen jam’iyyar ADC a jihar Sokoto.
ADC ta yi gangami a Sokoto domin kaddamar da yakin neman zaben Atiku Abubakar bayan an yi ta kai ruwa rana a tsakiyar makon nan.

Source: Twitter
Gwamnatin Sokoto ta hana 'yan ADC kamfe
Tashar Arise TV ta daura bidiyon Alhaji Kashim Ibrahim Imam yana mai bayanin yadda gwamnatin APC ta nemi hana su kamfe a X.

Kara karanta wannan
“Ko zai shafi Tinubu a 2027?” Yadda al’ummar Legas suka tarbi Kwankwaso ya ja hankali
Darekta Janar na kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar, Kashim Ibrahim Imam ya zargi gwamnatin APC da muzguna masu a Sokoto.
Kashim Imam ya zargi gwamnan Sokoto da hana su wurin da za su yi taron kamfe na ADC a jihar.
Saboda haka ne Atiku Abubakar mai neman zaba shugaban kasa a jam’iyyar ADC ya ce ya zama dole su fita tituna su nemo filin gangami.
“An hana mu wurin taro, shugaban kasarmu ya ce idan ta kama za mu yi gangamin a kan tituna ne, dole sai mun zo Sokoto.”
Samun otel a Sokoto ya gagari shugabannin ADC
Baya ga wurin taro, Kashim Imam ya ce an hana otel su ba ‘yan jam’iyyar ADC dakunan kwana, sannan aka hana su samun abubuwan hawa.
“Mun biya otel, amma aka umarci masu dakunan sun maido mana kudinmu. Shugaban kasarmu ya ce ba shakatawa muka zo yi a Sokoto ba. Idan ta kama mu kwana a motocinmu, mu kwana a gidajen abokanmu, sai mun zo Sokoto.
'Yan acaba da kabu-kabu sun je hutu
Jigon na ADC ya fada wa taron magoya bayansu cewa har ‘yan acaba an yi masu kashedi game da fita zirga-zirga lokacin da suka zo yin kamfe.
A dalilin hakan sai dai wasu ‘yan adawan suka kwana a gidajen abokansu. An kuma ji labari cewa sai a ranar wasunsu suka zo garin Sokoto.
Idan zargin ya tabbata, gwamnati ta biya ‘yan acaba da masu abubuwan hawa na haya kudi domin su zauna a gida, ka da su fita aiki a ranar.
Amma Darektan yakin zaben na Atiku Abubakar ya ce mutane sun zo taron ADC a kafa daga kauyuka da kananan hukumomin jihar Sokoto.
Darekta Janar ya sha alwashin ganin bayan Tinubu
Babban ‘dan siyasar suruki ne ga Atiku Abubakar kamar yadda jaridar The Africa Report ta taba fada.
Ya yi tunkaho da cewa a hakan, taron su ya yi armashi fiye da wanda APC ta shirya a garin Kaduna.
Fiye da shekaru 40 kenan, Kashim ya ce yana siyasa kuma duk wanda ya mara wa baya sai da yayi nasara a zaben shugaban kasa tun 1992.
Don haka wannan karo ya ce da yardar Allah SWT Atiku za iyi waje da shugaba Bola Tinubu a 2027.
Atiku Abubakar ya zargi DSS da shirin zanga-zanga
Ana da labari DSS ta bayar da umarnin bincike kan zargin Atiku Abubakar cewa ana shirin tayar da zanga-zanga a Sakkwato.
DSS ta musanta zargin, amma ta ce za ta gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Duk da wannan zargi, magoya baya sun yi tattaki da kafafunsu kuma sun samu halartar gagarumin taron yakin zaben ADC.
Asali: Legit.ng

