2027: Kotu Ta Rusa Takarar Atiku da Dukkan 'Yan ADC a Najeriya

2027: Kotu Ta Rusa Takarar Atiku da Dukkan 'Yan ADC a Najeriya

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta rusa shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark
  • Kotun ta soke duk matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takara
  • Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar ADC ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, tare da rusa duk matakan da suka ɗauka a madadin jam’iyyar.

Hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke a ranar Alhamis ya haɗa da soke zaɓen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

ADC ta kawar da shakku, ta bayyana wurin kaddamar da kamfen din Atiku a Sokoto

Manyan ADC da Nafiu Bala
David Mark, Nafiu Bala da David Mark. Hoto: ADC Vanguard
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta saurari ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa mai kula da Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar.

Kotu ta rusa shugabancin David Mark

A hukuncin nata, kotun ta bayyana kwamitin riƙon ƙwarya na ADC ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark a matsayin wanda bai halatta ba.

Kwamitin ne ya shirya zaɓen fitar da gwani da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Nafiu Bala Gombe ya shigar da ƙarar ne domin ƙalubalantar tsarin da kwamitin David Mark ya bi wajen karɓar shugabancin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Chief Ralph Nwosu, shi ne ya cancanci ya karɓi ragamar shugabancin ADC.

ADC ta ce za ta ɗaukaka ƙara

Bayan hukuncin, Punch ta wallafa cewa jam’iyyar ADC ta bayyana aniyarta ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar matakin kotun.

Kara karanta wannan

Duk da zargin barazana, Atiku zai kaddamar da yakin neman zabensa a Sokoto

Sakataren jin daɗin walwala na jam’iyyar na ƙasa, Nkemakolam Ukandu, wanda daga baya aka shigar a shari’ar a matsayin mai ruwa da tsaki, ya ce za su garzaya kotun ɗaukaka ƙara.

Hukuncin na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan Atiku Abubakar ya gudanar da gagarumin gangamin neman zaɓe a Jihar Sokoto domin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku Abubakar da 'yan ADC
'Yan Tinubu Must Go da Atiku Abubakar. Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

Tun da farko, hukumar INEC ta wallafa sunan Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, kuma ya zaɓi tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.

Sarkin Musulmi ya karɓi Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna.

Sarkin ya yi kiran ne lokacin da ya karɓi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa da ke Sokoto.

Atiku ya gode wa Sarkin Musulmi bisa kyakkyawar tarbar da ya yi masa, tare da jaddada muhimmancin rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng