Atiku da Amaechi Sun Dura Jihar Sakkwato domin Kaddamar da Yakin Neman Zaben ADC

Atiku da Amaechi Sun Dura Jihar Sakkwato domin Kaddamar da Yakin Neman Zaben ADC

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, sun isa Sakkwato domin ƙaddamar da yakin neman zabe
  • Isowar Atiku ta haddasa cunkoson ababen hawa a manyan tituna da kewayen shiga birnin Sakkwato
  • An tura jami’an tsaro zuwa muhimman wurare yayin da ake fargabar rikici kan rufe ofishin kamfen jam’iyyar ADC da zargin kai hare-hare ga magoya bayanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, abokin takararsa, Rotimi Amaechi, da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar sun isa Jihar Sakkwato.

Hakan na zuwa ne yayin da Atiku Abubakar ke shirin ƙaddamar da yakin neman zabensa a babban zaben shugaban kasa na 2027.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar lokacin da ya isa jihar Sakkwato Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Atiku da Amaechi ya isa Sakkwato

Daily Trust ta rahoto cewa Atiku da Amaechi sun iso ne a jiragen sama daban-daban, inda tsohon Ministan Sufuri, Amaechi, ya sauka kafin ɗan takarar shugaban ƙasar ya karasa.

Kara karanta wannan

Duk da zargin barazana, Atiku zai kaddamar da yakin neman zabensa a Sokoto

A halin yanzu, suna kan hanyarsu ta zuwa sakatariyar ADC ta jihar Sokoto da ke kan titin Ilorin, cikin ayarin motocin da magoya baya ke rakiyarsu, suna ɗauke da tutocin jam’iyyar da fastocin kamfen.

Zuwan tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya haddasa cunkoson ababen hawa a tituna da kewayen ƙofar Sakkwato, yayin da magoya bayansa suka fito domin tarbarsa.

Jaridar Leadership ta gano cewa bikin ƙaddamar da kamfen ɗin zai gudana ne da ƙarfe 5:000 na yamma a ofishin ADC da ke Sakkwato.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake fama da tashin hankali kan rufe ofishin kamfen ɗin jam’iyyar ADC da kuma zargin kai hare-hare ga magoya bayanta cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

ADC ta dage kan kaddamar da kamfe

Duk da wannan lamari, shugaban ADC na jihar, Alhaji Bello Muhammad Goronyo, ya dage cewa za a gudanar da taron kamar yadda aka tsara. Ya bayyana rufe ofishin a matsayin “ƙoƙarin tsoratar da ’yan adawa”.

Kara karanta wannan

ADC na neman darewa saboda takarar Atiku a 2027? An ji yadda zancen yake

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar manyan jiga-jigan jam’iyyar, ciki har da tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, Sanata Abdul Ningi da ɗan takarar gwamnan ADC a jihar, Hon. Manir Muhammad Dan’iya.

Legit Hausa ta gano cewa an tura jami’an tsaro zuwa muhimman wurare a cikin birnin Sakkwato domin tabbatar da zaman lafiya da kiyaye doka da oda.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da gudanar da taron cikin kwanciyar hankali.

ADC, wadda gamayyar shugabannin jam’iyyun adawa suka yi hadaka a ciki, ta zaɓi Sakkwato a matsayin ɗaya daga cikin jihohin farko da za ta ƙaddamar da kamfen ɗin takarar shugaban ƙasa a shiyyar Arewa maso Yamma.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262