APC Ta Ba ADC Mafita kan Rusa Takarar Atiku da Kotu Ta Yi
- Jam’iyyar APC ta bukaci bangaren ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark ya magance rikicin cikin gida maimakon zargin jam’iyyar mai mulki
- APC ta ce ba ta da hannu a shari’ar da ta kai ga tsige shugabancin bangaren Mark, tana mai cewa rikicin na cikin gida ne na ADC
- Jam’iyyar ta kuma zargi David Mark da abokan tafiyarsa da karbe ikon ADC domin biyan bukatar Atiku Abubakar ta neman shugabancin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jam’iyyar APC ta bukaci bangaren jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark ya gyara rikicin cikin gida, bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke shugabancinsa.
APC ta ce ba ta da hannu a shari’ar, inda ta bukaci shugabannin bangaren su daina zargin jam’iyyar mai mulki da kuma sukar bangaren shari’a.

Source: Twitter
A wata sanarwa da kakakin APC na kasa, Felix Morka, ya fitar ranar Juma’a a Abuja, Vanguard ta rahoto ya ce babu wata alaka tsakanin jam’iyyarsa da shari’ar da ta kai ga hukuncin kotun.
APC ba ta da hannu a rikicin ADC
Morka ya bayyana cewa APC ba ta cikin wadanda suka shigar da kara ko wadanda ake kara a shari’ar, don haka ba ta da rawar da ta taka wajen hukuncin.
Ya ce shari’ar ta samo asali ne daga karar da wasu jami’an ADC na kasa suka shigar kan bangaren da David Mark ke jagoranta.
Kakakin APC ya bayyana karar a matsayin rikicin da shugabannin ADC suka shigar kan wasu shugabannin jam’iyyar, yana mai cewa bai kamata a daura wa APC alhakin abin da ya faru ba.
APC ta zargi David Mark da kuskure
Morka ya zargi David Mark da abokan tafiyarsa da karbe ikon ADC domin biyan bukatar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na neman zama shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan
Sanata Dino Melaye ya jagoranci yi wa Tinubu 'Allah Ya isa' ƙafa 3 a gangamin ADC
Ya ce kotu mai hurumi ta tabbatar da cewa yadda suka karbe shugabancin jam’iyyar ya saba wa doka da tsarin dimokuradiyyar cikin gida na ADC.

Source: Twitter
A cewarsa, bangaren na Mark yana sukar APC da bangaren shari’a duk lokacin da hukuncin kotu bai yi masa daidai ba, amma idan hukuncin ya amfane shi, sai ya yaba wa tsarin shari’a.
Kakakin APC ya ce hukuncin kotun ya nuna muhimmancin bin doka da kuma 'yancin bangaren shari’a a Najeriya.
Ya kuma zargi shugabannin bangaren ADC da rashin daukar alhakin rikicin da suka jawo wa kansu, yana mai cewa kotu ta tabbatar da sakamakon ayyukansu.
Obi ya goyi bayan Atiku
A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi, ya nuna damuwa kan hukuncin kotun da ya soke zaben Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027.
Obi ya ce hukuncin na iya jefa jam’iyyun adawa cikin rashin tabbas gabanin babban zaben, tare da rage damar masu zabe na zabar shugabannin da suke so.
Tsohon gwamnan ya kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da amfani da dabarun siyasa wajen raunana jam’iyyun adawa da hana su gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
Asali: Legit.ng
