"Ko a Jiki Na," Atiku Ya Maida Martani bayan Kotu Ta Rushe Takararsa a Zaben 2027

"Ko a Jiki Na," Atiku Ya Maida Martani bayan Kotu Ta Rushe Takararsa a Zaben 2027

  • Atiku Abubakar ya zargi masu ƙulla makircin siyasa da amfani da hukuncin kotu wajen raunana ADC da kawo cikas ga takararsa
  • Ya ce hukuncin ya zo ne kwana guda bayan dimbin jama’a sun fito tarbarsa a Sokoto yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar
  • Ɗan takarar shugaban ƙasar ya yi kira ga magoya bayan ADC su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da yaɗa saƙon jam’iyyar cikin lumana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da hukuncin kotu wanda ya rusa shugabancin Sanata David Mark.

Wazirin Adamawa ya bayyana matakin a matsayin wani shiri na musamman domin raunana ADC da kawo cikas ga takararsa.

Atiku.
"Ko a jiki na," Atiku Ya Yi Martani kan Hukuncin Kotu da Ya Rusa Takararsa
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na ADC, ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso

Atiku ya kafa misali da taron Sokoto

Atiku ya ce lokacin da aka yanke hukuncin ya nuna cewa akwai abin lura a cikinsa, inda ya ce hukuncin ya zo ne kwana guda bayan dubban magoya baya da jama’a sun fito a Sokoto domin tarbarsa da halartar ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ADC.

Atiku ya ce taron ya nuna shirin al’ummar yankin Arewa na neman sauyi, yana mai cewa jama’ar Sokoto sun fito ne saboda halin tsadar rayuwa da kuma amincewarsu da alƙawarin da jam’iyyar ta yi na dawo da sauƙin rayuwa.

“Dubban mutanen Sokoto sun fito saboda suna manufarsu ta neman sauyi kuma sun yi imani da alƙawarinmu na dawo da sauƙin rayuwa.
"Abin da muka gani a Sokoto farkon abin da ke tafe ne kawai. Al’ummar Kebbi ma za su bayyana ra’ayinsu, haka kuma ’yan Najeriya a faɗin ƙasar yayin da yaƙin neman zaɓenmu ke ci gaba,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

Atiku ya kuma zargi jam’iyya mai mulki da ƙoƙarin raunana goyon bayan da yake da shi a Arewa tare da kawo cikas ga yaƙin neman zaɓensa, wanda ya ce saƙonsa na samun karɓuwa a sassan ƙasar.

Atiku ya yi martani kan hukuncin kotu

Ɗan takarar shugaban ƙasar ya kuma ce hukuncin da kotu ta yanke ya haifar da wasu muhimman tambayoyi na shari’a.

Ya bayyana cewa Mai Shari’a Musa Liman na babbar kotun tarayya ɗaya da ke Abuja ya taɓa yin watsi da ƙarar da aka shigar don kalubalantar shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark a ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/1637/2025.

Atiku ya tambayi dalilin da ya sa aka sake shigar da wata ƙara domin buɗe irin wannan takaddama bayan an riga an yanke hukunci a kanta.

Ya bayyana sake shigar da ƙarar a matsayin yunƙurin kauce wa hukuncin kotu da yake nan daram, yana mai cewa za su ƙalubalanci wannan mataki a Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar ya isa birnin Kebbi Hoto: Atiku Network
Source: Facebook

Atiku ya kwantar da hankulan jama'a

Atiku ya yi kira ga magoya bayan ADC da su kwantar da hankalinsu, su kiyaye doka, kuma kada su bari hukuncin ya rage musu ƙwarin gwiwar da suka samu bayan gangamin Sokoto.

Kara karanta wannan

2027: Sarkin Musulmi ya gana da Atiku da manyan ADC a Sokoto

Ya ce tawagar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ta riga ta isa Jihar Kebbi, kuma za ta ci gaba da kai saƙonta zuwa sauran sassan Najeriya.

“Mun buƙaci magoya bayanmu da kada su girgiza, su riƙa kai saƙonmu gida-gida, sannan su kasance cikin lumana da mayar da hankali. Babu abin da zai girgiza mu,” in ji shi.

ADC ta yi fatali da hukuncin kotu

Kun ji cewa jam’iyyar ADC ta yi martani bayan babbar kotun tarayya ta soke shugabancinta da takarar Atiku Abubakar.

Jam’iyyar ta ce hukuncin bai shafi makomarta kadai ba, illa har da makomar dimokuradiyya a Najeriya, tana mai cewa za ta daukaka kara zuwa kotun gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262