EFCC: Yadda Kwankwaso da Abba Kabir ke Kai Ruwa Rana ana Shirin 2027
- Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa wajen kai masa hari ta fuskar siyasa
- Gwamnatin Kano ta musanta zargin, tana mai cewa Gwamna Abba ba shi da hannu a binciken da EFCC ke yi wa Kwankwaso.
- Kwankwaso ya kuma zargi gwamnan da ƙoƙarin yin tasiri ga INEC da ɓangaren shari’a domin hana bayyana sunan ɗan takarar NDC na gwamna a Kano, Aminu Gwarzo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa wajen ɓata masa suna da kai masa hari ta fuskar siyasa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta maida martani kan zarge zargen da Kwankwaso ya yi wa Gwamna Abba
Kwankwaso, wanda yake mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, ya yi zargin ne a wani saƙo da ya wallafa a ranar Juma’a.

Source: Facebook
Sai dai Punch ta rahoto gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin, tana mai cewa gwamnan ba shi da hannu a binciken da EFCC ke yi wa tsohon gwamnan.
Zargin Kwankwaso kan Abba
Tsohon gwamnan ya yi zargin cewa Abba Yusuf ne da kansa ya shigar da ƙara ga EFCC watanni da suka gabata domin hukumar ta bincike shi.
Ya ce Abba ya taɓa yi masa aiki a matsayin mataimaki na musamman, babban sakataren ofishinsa da kwamishina, sannan shi ne ɗan takarar da ƙungiyar Kwankwasiyya ta tsayar a zaɓen gwamnan Kano na 2019 da 2023.
Kwankwaso ya bayyana cewa sun daɗe suna hulɗa tsawon shekaru 43, kuma ya amince da shi sosai har ya ba shi damar sanin muhimman bayanai game da shi.
Sai dai ya ce amincewar da ya yi wa gwamnan ta zama abin da aka yi amfani da shi ta hanyar da bai dace ba.
Abba ya musanta zargin
A martaninta, gwamnatin jihar Kano ta bayyana zargin Kwankwaso a matsayin abin ruɗarwa da kuma wanda siyasa ta sa aka yi shi.
The Cable ta wallafa cewa Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Sunusi Tofa, ne ya fitar da sanarwar martanin a ranar Juma’a.
Gwamnatin ta ce Gwamna Abba Yusuf ba shi da hannu a duk wata mu’amala da Kwankwaso yake yi da EFCC.
Ta ƙara da cewa Kwankwaso ya daɗe yana hulɗa da hukumar tun kafin kafa gwamnatin Abba Yusuf, don haka ba daidai ba ne a danganta gwamnan da wani al'amari da ya faru kafin hawansa mulki.
Yadda rikicinsu ya fara a Kano
Rikicin ya ƙara fito da sabanin siyasa tsakanin mutanen biyu, waɗanda a baya suke manyan aminai a ƙungiyar Kwankwasiyya da Kwankwaso ke jagoranta.

Kara karanta wannan
"Babban ƙalubalen da Peter Obi da Kwankwaso za su fara tunkara idan suka ci zaben 2027"
Abba ya fice daga jam’iyyar NNPP ranar 23 ga Janairu, 2026, sannan ya koma APC a hukumance bayan kwana uku, yana mai cewa rikice-rikicen cikin gida da sabanin shugabanci ne suka sa ya ɗauki matakin.

Source: Facebook
Wasu zaɓaɓɓun jami’ai, ciki har da ’yan majalisar dokokin Kano da na tarayya, sun bi shi zuwa APC.
A wata tattaunawa a baya-bayan nan, Abba ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ne ya fara tattauna yiwuwar komawa APC, har ya ƙarfafa shi ya yi shawarwari da fadar shugaban ƙasa.
Sai dai ƙungiyar Kwankwasiyya ta ƙaryata wannan ikirari, tare da ƙalubalantar gwamnan da ya gabatar da hujjar abin da ya faɗa.
Ana zaben gwaji a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shirya gudanar da gwajin amfani da na’urorin tantance masu zaɓe da tura sakamakon zaɓe a ranar 28 ga Nuwamba, 2026.
Za a gudanar da gwajin a rumfunan zaɓe 17,676 a faɗin Najeriya domin tantance ingancin na’urar BVAS da tsarin aika sakamakon zaɓe ta intanet.
Hukumar ta buƙaci masu katin zaɓe da ke rumfunan da aka zaɓa su halarci gwajin domin taimaka mata gano matsalolin da ka iya tasowa kafin zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
