Nafiu Bala Ya Fito Yana Murna da Rusa Takarar Atiku da Dukkan 'Yan ADC a Najeriya
- Nafiu Bala da ke ikirarin shi ne sahihin shugaban jam’iyyar ADC, ya yi murnar hukuncin kotu da ya soke shugabancin Sanata David Mark
- Hukuncin kotun ya kuma rusa matakan da shugabancin Mark ya ɗauka, lamarin da ka iya shafar takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a jam’iyyar
- Sai dai wasu jiga-jigan ADC da magoya bayan Atiku sun yi martani daban-daban kan hukuncin, inda wasu suka nuna rashin amincewa da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Nafiu Bala, wanda ke ikirarin shi ne sahihin shugaban jam’iyyar ADC, ya bayyana farin cikinsa bayan wata kotu ta soke shugabancin Sanata David Mark da matakan da ya ɗauka a madadin jam’iyyar.
Bayan sanar da hukuncin, Nafiu ya wallafa kalaman godiya ga Allah a shafinsa na sada zumunta, inda ya rubuta sau uku cewa: “Alhamdulillah.”

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa hukuncin ya haifar da martani daga wasu jiga-jigan jam’iyyar da magoya bayan Atiku Abubakar, musamman ganin tasirin da zai iya yi kan shirin ADC na zaɓen 2027.
Nafiu Bala ya gode wa Allah
A sakon da ya wallafa a Facebook, Nafiu Bala ya nuna farin cikinsa bayan kotun ta amince da buƙatunsa na rusa matakan da shugabancin David Mark ya ɗauka a madadin ADC.
A sakon da ya wallafa bayan hukuncin, ya rubuta: “Alhamdulillah, alhamdulillah, alhamdulillah”, wanda ke nuna godiyarsa ga Allah bisa hukuncin da kotun ta yanke.
A wani martani, ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan ADC, Uche Diala, ya bayyana cewa jam’iyyar na nan kan matsayinta na goyon bayan David Mark a matsayin shugabanta da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.
A sakon da ya wallafa a Facebook, Diala ya ce babu wani abu da zai raba hankalin jam’iyyar ko jawo tashin hankali a cikinta.
Martanin mutanen Atiku
Abdulrashid Shehu, wanda ke aiki a matsayin hadimin Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan hukuncin da cewa jam’iyyar APC na cikin fargaba a sakon da ya wallafa a X.
Shi kuwa Aminu Kankia ya nuna damuwarsa kan abin da ya kira ƙoƙarin hana Atiku samun tikitin takarar shugaban ƙasa.
Kankia ya yi zargin cewa hana Atiku tikitin ADC ba siyasa ba ce, illa matakin da ka iya jefa ƙasar cikin rikici da lalacewa.

Source: Facebook
A nasa martanin, Ibrahim Di Adams ya nuna zargin cewa abin da ya faru na iya kasancewa aikin jam’iyyar mai mulki ne.
Bwuna Junior kuwa ya ce kotun koli za ta iya sauya hukuncin da aka yanke, yana mai nuna cewa shari’ar ba ta ƙare ba.
Atiku ya ziyarci Sarkin Musulmi
A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna.
Sarkin ya yi kiran ne lokacin da ya karɓi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa da ke Sokoto.
Atiku ya gode wa Sarkin Musulmi bisa kyakkyawar tarbar da ya yi masa, tare da jaddada muhimmancin rawar sarakunan gargajiya wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Asali: Legit.ng


