Ziyarar da Kwankwaso Ya Kai Legas na Iya Zama Barazana ga Tinubu a Zaben 2027? An Samu Bayanai

Ziyarar da Kwankwaso Ya Kai Legas na Iya Zama Barazana ga Tinubu a Zaben 2027? An Samu Bayanai

  • Dandazon mutanen da suka fito lokacin da dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso ya kai ziyara Legas ya tada kura
  • Wasu mazauna Legas sun yi watsi da ikirarin cewa Kwankwaso na iya zama barazana ga kuri'un Tinubu zai samu a jihar a zaben 2027
  • Wasu ‘yan kasuwa sun ce suna maraba da Kwankwaso, amma hakan ba yana nufin za su zabe shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Wasu masu kada kuri’a a Jihar Legas sun yi watsi da ziyarar dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya kai jihar a ranar Alhamis.

Hakan dai ya biyo bayan yawan mutanen da Kwankwaso ya tara lokacin da ya ziyarci yankin da Hausawa, Fulani da Ibo suka fi yawa.

Kara karanta wannan

Sanata Dino Melaye ya jagoranci yi wa Tinubu 'Allah Ya isa' ƙafa 3 a gangamin ADC

Kwankwaso.
Dan takarar mataumakin shugaban kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a taron magoya bayan jam'iyyarsa Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Leadership ta ce a yayin ziyarar, tawagar NDC ta je shahararrun kasuwannin Ilepo da Kontagora da ke Karamar Hukumar Alimosho, tare da dan takarar gwamnan jam’iyyar a Legas, Mista Funso Doherty.

Ziyarar Kwankwaso ta zama abin ce-ce-ku-ce a siyasa saboda yana takarar mataimakin shugaban kasa tare Mista Peter Obi, wanda a zaben 2023 ya samu kuri’u 582,454 a Legas, yayin da Bola Tinubu na APC ya samu kuri’u 572,606.

Ra’ayoyin mazauna Legas

Da yake mayar da martani kan ziyarar Kwankwaso zuwa yankunan da aka yi masa tarba mai kyau, Mista Ajayi Segun ya ce dan siyasar ya dade yana da alaka da ‘yan kasuwar yankin.

Ya ce:

“Sanata Rabiu Kwankwaso shi ne jagoran tafiyar Kwankwasiyya, wata babbar kungiyar siyasa da aka sani a fadin kasar nan. Shi gogaggen dan siyasa ne da ya gina alaka a sassa daban-daban na kasar.
“A wannan karon yana takara tare da Peter Obi, wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Jihar Legas a 2023. Abin da ya kamata ku sani shi ne, yanayin siyasa a jihar ya sauya tun daga wancan lokacin. Yarabawa ba za su sake bari hakan ta faru ba a Legas. Zaben 2023 ya zo musu a bazata.

Kara karanta wannan

Atiku ya soki DSS, ya fadi makircin da aka shirya domin hana shi gangamin kamfe a Sokoto

“A gaskiya, idan ba za ku zabi APC, wato jam’iyyar shugaban kasa ba, watakila sai kun yi taka-tsantsan a rumfar zabensa a babban zaben 2027. Don haka, ba zai yiwu Peter Obi ya yi nasara ba.”

A nasa bangaren, Haruna Abdulahi, wani dan kasuwa a Kasuwar Ilepo, ya ce suna kaunar Kwankwaso kuma suna kallonsa a matsayin jagoransu, amma tarbar da suka yi masa ba ta nufin duk wadanda suka fito za su zabe shi.

Jam'iyyar APC ta yi martani

A gefe guda, jam’iyyar APC ta Jihar Legas ta yi watsi da ikirarin cewa NDC, karkashin jagorancin Peter Obi da Kwankwaso, za ta kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 a jihar.

Kakakin APC a Legas, Hon. Seye Oladejo, ya ce zaben shugaban kasa na 2023 ya wuce, don haka bai kamata a rika amfani da sakamakonsa wajen hasashen duk wani zabe na gaba ba.

Ya bukaci ‘yan siyasa da su guji mayar da siyasar Legas kan lissafin kabilanci, yana mai cewa jihar al’umma ce mai cike da mutane daga kabilu da addinai daban-daban.

Kwankwaso ya ja hankalin Atiku

Kun ji cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya ce bai kamata Atiku Abubakar ya karya tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu ba.

Kwankwaso ya buƙaci Atiku ya mara wa Peter Obi baya domin Kudu ta kammala wa’adin mulkin da ya rage mata kafin shugabancin ya koma Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262