Hukuncin Kotu: Adawa Ta Kara Karfi, Jam'iyyun Siyasa 6 Sun Goyi Bayan ADC da Atiku
- Jam'iyyar ADC da dan takararta na shugaban kasa na ci gaba da samun goyon bayan bayan hukuncin babbar kotun tarayya
- Jam'iyyun siyasa 9 sun bayyana hukuncin kotun da ya rushe shugabancin David Mark a ADC a matsayin barazana ga dimokuradiyya
- Sun yi gargadin cewa abin da ya faru da ADC a yau zai iya faruwa da kowace jam’iyyar adawa a gobe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jam’iyyun adawa tara karkashin kungiyar Coalition for Democracy sun nuna goyon bayansu ga jam’iyyar adawa ta ADC.
Jam'iyyun sun bayyana hukuncin da Babbar Kotun Tarayya na rushe shugabancin ADC karkashin Sanata David Mark da kuma soke takarar Atiku Abubakar a matsayin “wani mummunan mataki na kawar da yan adawa."

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Salihu Moh. Lukman ya sanya wa hannu a madadin jam’iyyun da ke cikin hadakar.

Kara karanta wannan
Sanata Dino Melaye ya jagoranci yi wa Tinubu 'Allah Ya isa' ƙafa 3 a gangamin ADC
Ƙungiyar ta yi gargadin cewa abin da ke faruwa da ADC a yau zai iya faruwa da kowace jam’iyyar adawa a gobe.
Jam’iyyun da ke cikin hadakar
An kafa kungiyar Coalition for Democracy ne bayan taron G100 Opposition Summit da aka gudanar a Abuja ranar 31 ga Agusta, 2026.
Jam’iyyun da ke cikinta sun hada da ADC, APM, DLA, NRM, NDC, PDP, PRP, SDP da kuma YPP.
Kungiyar ta bayyana kanta a matsayin hadakar da aka kafa domin kare dimokuradiyya, kare tsarin siyasar da ke bai wa jam’iyyu daban-daban damar fafatawa, da kuma tabbatar da gudanar da zabuka cikin ’yanci, adalci, gaskiya da gasa ta hakika.
Hadakar ta tuna cewa kwana daya kacal kafin hukuncin kotun, ta riga ta yi gargadi kan yadda damar gudanar da harkokin dimokuradiyya a Najeriya ke kara raguwa.
Ta ce a lokacin ta nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa magoya bayan jam’iyyun adawa, hana gudanar da tarukan siyasa da kuma "amfani da hukumomin gwamnati a matsayin makami wajen murkushe abokan hamayyar siyasa.”
Gargadi kan barazana ga adawa
Sanarwar ta ce:
“Idan ana kai wa jam’iyyun adawa hari a kan tituna, hukumomin gwamnati na kawo musu cikas, sannan kuma ana barazanar kawar da su ta hanyar hukunce-hukuncen kotu, ya kamata ’yan Najeriya su tambayi kansu ko har yanzu jam’iyya mai mulki tana da niyyar fuskantar wata jam'iyyar adawa a rumfunan zabe.”
Kungiyar ta ce tana mutunta ’yancin bangaren shari’a da kuma damar duk wanda bai gamsu da wani hukunci ba na neman hakkinsa ta hanyoyin doka.

Source: Twitter
Sai dai ta dage cewa bai kamata kotuna su zama hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen fafatawar siyasa ba.
Kungiyar ta bayyana goyon bayanta ga ADC a matakin da jam’iyyar ta dauka na kalubalantar hukuncin kotun ta hanyar hanyoyin shari’a da suka dace.
ADC za ta ɗaukaka kara
Kun ji cewa jam’iyyar ADC ta yi martani bayan babbar kotun tarayya ta soke shugabancinta da takarar Atiku Abubakar, tana mai zargin APC da kokarin jefa Najeriya cikin rikici.
Jam’iyyar adawan ta yi watsi da hukuncin kotun tare da bayyana cewa za ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara
Asali: Legit.ng
