Zazzafan Martanin da ADC Ta Yi bayan Kotu da Rusa Takarar Atiku, Shugabanninta
- Jam’iyyar ADC ta yi martani bayan babbar kotun tarayya ta soke shugabancinta da takarar Atiku Abubakar
- Jam’iyyar ta yi watsi da hukuncin kotun tare da bayyana cewa za ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara
- ADC ta kuma yi barazanar kai korafi ga majalisar kula da harkokin shari’a ta kasa kan yadda aka gudanar da shari’ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi magana kan hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Hukuncin wanda ya soke shugabancinta tare da rushe takarar Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2027.
Hakan na cikin wata sanarwa mai zafi da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis wanda aka wallafa a X.
ADC ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da kokarin jefa Najeriya cikin rikici ta hanyar amfani da kotuna.

Kara karanta wannan
Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya
Jam’iyyar ta ce hukuncin bai shafi makomarta kadai ba, illa har da makomar dimokuradiyya a Najeriya.
Ta bayyana cewa hukuncin babbar barazana ce ga zaman lafiyar siyasa da kuma sahihancin tsarin zabe a kasar.
ADC ta ce APC na kokarin raunana 'yan adawa
A cewar jam’iyyar, abin da ya faru a kotu wani bangare ne na shirin kai wa jam’iyyun adawa hari ta hanyar shari’a gabanin babban zaben 2027.
ADC ta ce:
“Muna da dalilan da suka sa muka yi imanin cewa an dade da rubuta hukuncin wannan shari’a. Gangamin Sokoto ne kawai ya zama dalilin gaggauta yanke hukuncin.
“A jiya, dubban daruruwan 'yan Najeriya sun fito domin nuna goyon bayansu ga ADC da alkawarinmu na samar musu da rayuwa mai sauki.”
Ta ce abin takaici ne yadda a yau ake sanar da mutanen cewa za a iya soke jam’iyyar da 'yan takarar da suka nuna wa goyon baya ta hanyar alkalami daya.
Sai dai APC ta sha musanta zargin cewa tana kokarin raunana jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027.
Abin da kotu ta yanke kan shugabancin ADC
Sanarwar ADC ta zo ne sa'o'i kadan bayan Mai Shari’a Peter Lifu ya soke kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata David Mark.
Kotun ta bayyana kwamitin a matsayin wanda ba shi da hurumin gudanar da ayyukan jam’iyyar, tare da soke dukkan matakan da ya dauka.
Wannan ya hada da zaben fidda gwani da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC a zaben 2027.
Haka kuma, kotun ta umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kada ta amince da matakan da aka dauka a taron kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar karo na 99, wanda aka gudanar a ranar 27 ga watan Yulin 2025.
Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, ne ya shigar da karar yana kalubalantar yadda David Mark da sauran mutane suka karbe shugabancin ADC.
ADC ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin
Kafin yanke hukuncin, INEC ta riga ta wallafa sunan Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na ADC.

Kara karanta wannan
Kotu ta soke tikitin ɗan takarar gwamna a 2027, ta umarci a sake zaben fitar da gwani
Atiku ya kuma zabi tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takararsa.
Hukuncin kotun ya zo ne kasa da sa'o'i 24 bayan Atiku ya gudanar da gangamin yakin neman zabe a jihar Sokoto.
Sai dai ADC ta dage cewa tikitin takararta yana nan daram har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan karar.
Sakataren walwalar jam’iyyar na kasa, Nkemakolam Ukandu, ya ce za su kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara, kuma ba za su mika wa wani hakkinsu ta bayan fage ba.
ADC ta bukaci mambobinta su kwantar da hankalinsu
Jam’iyyar ta bukaci mambobinta da su kwantar da hankulansu tare da kasancewa cikin hadin kai duk da hukuncin kotun.
Ta ce babu wani hukuncin kotu da ta yi zargin an samu ta hanyar amfani da siyasa da zai iya dakile muradin 'yan Najeriya da ke son sauyi a zaben 2027.
Karin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng
