Gaskiya Za Ta Yi Halinta: Hukumar DSS Ta Fara Bincike kan Zargin da Atiku Abubakar Ya Yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
- Hukumar DSS ta ƙaddamar da bincike kan zargin Atiku Abubakar cewa jami’anta sun shirya shirya zanga-zanga a Jihar Sakkwato
- Hukumar ta ce jami’anta sun ceci ɗan takarar gwamnan ADC, Mannir Dan’iya, yayin harin da aka kai masa a ranar 31 ga Oktoba, 2026
- DSS ta ce ta naɗa jami’an bincike kan zargin ne domin girmama tsohon mataimakin shugaban ƙasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi cewa hukumar ta shirya zanga-zanga a Jihar Sakkwato.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya zargi hukumar DSS da ƙulla makircin shirya zanga-zanga a jihar Sakkwato domin hana taron kaddamar da kamfe dinsa.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Mai garkuwa da mutane ya shiga hannu yana kokarin karbar kudin fansa

Source: Twitter
DSS ta musanta zargin shirya zanga-zanga
Leadership ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, DSS ta ce zargin ya saɓa wa ayyukan da take gudanarwa na kare ’yan siyasa ba tare da la’akari da jam’iyyun da suke ciki ba.
Sanarwar, wadda Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Sadarwa, Favour Dozie, ya sanya wa hannu, ta ce jami’an DSS da aka tura domin kare ɗan takarar gwamnan ADC a Jihar Sakkwato, Mannir Dan’iya, sun cece shi daga harin da aka kai masa.
Ta ƙara da cewa an yi wa jami’an DSS biyu duka a yayin lamarin, kuma har yanzu suna karɓar magani a asibiti.
A cewar hukumar, Dan’iya da kansa ya kira Daraktan DSS na Jihar Sakkwato domin gode wa jami’an bisa matakin da suka ɗauka na ceto shi, tare da neman a ƙara tura masa jami’an tsaro.
DSS ta fara bincike kan zargin Atiku
DSS ta ce lamarin ya nuna irin ƙudurin da take da shi na kare ’yan siyasa ba tare da la’akari da jam’iyyun da suke wakilta ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Kebbi: Gwamnati ta yi maganar ‘rusa’ ginin tsohon ministan Buhari, Abubakar Malami
Sai dai hukumar ta ce zargin da Atiku ya yi na iya raunana karfin gwiwar jami’an da ke sadaukar da rayukansu wajen gudanar da ayyukansu.
Duk da wannan matsaya, hukumar ta ce shugaban DSS ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin domin girmama tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Source: Facebook
DSS ta kuma tuna da wani makamancin zargi da ɗan takarar shugaban ƙasa na AAC, Omoyele Sowore, ya yi, inda ya zargi DSS da hannu a harin da aka kai masa a Jihar Ekiti.
DSS ta ce ta yi maraba da binciken da ’yan sanda suka gudanar kan lamarin. Ta ƙara da cewa rahoton farko ya nuna cewa rikici ne ya haddasa harin, kuma an kama mutane 11 da ake zargi da hannu a lamarin.
Wane zargi Atiku ya yi?
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa ya zargi shugabannin DSS da daukar mutane domin kawo cikas ga kaddamar da yakin neman zaben ADC a Sokoto.
Ya bayyana lamarin a matsayin wani shiri na musamman da aka tsara domin kawo cikas ga ADC da kuma hana ’yan Najeriya damar zabar shugabannin da suke so.
Asali: Legit.ng