Zaben 2027: Manyan Alkawuran Atiku ga 'Yan Najeriya a wajen Kamfen ADC a Sokoto
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur da buɗe iyakokin ƙasa domin halastaccen kasuwanci
- Atiku ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalar tsaro domin manoma su koma gonakinsu, musamman a yankunan da matsalar ta shafa
- Shugaban ADC, David Mark, ya ce yawan mutanen da suka halarci gangamin Sakkwato ya nuna cewa al’ummar jihar na son sauyin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur.
Atiku ya kuma yi alkawarin buɗe iyakokin Najeriya domin kasuwanci da ƙasashe maƙwabta, tare da magance matsalar tsaro idan ya lashe zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Atiku ya bayyana waɗannan alƙawura ne a ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2026 yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC a Sokoto, wanda ya samu halartar dubban magoya bayan jam’iyyar.
Ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen inganta tsaro, farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da kuma bunƙasa kasuwanci tsakanin Najeriya da ƙasashe maƙwabta.
Atiku Abubakar zai dawo da tallafin man fetur
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce zai buɗe dukkan iyakokin Najeriya na ƙasa domin bai wa ’yan kasuwa damar gudanar da halastaccen ciniki da sauran ƙasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
Ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka musamman ga al’ummomin Arewacin Najeriya da suka dogara da kasuwanci da ƙasashen da ke maƙwabtaka da su.
"Zan buɗe dukkan iyakokin ƙasa domin al’ummarmu su gudanar da halastaccen kasuwanci da ’yan’uwanmu da ke ƙetaren iyaka.
“Za mu dawo da tallafin man fetur, sannan mu yi duk abin da mutum zai iya yi domin kawo ƙarshen rashin tsaro, ta yadda al’ummarmu za su iya komawa gonakinsu.”
Ya buƙaci ’yan Najeriya su kare ƙuri’unsu
Atiku ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su fito su kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen 2027, tare da zaɓar ADC da kuma tabbatar da cewa an ƙirga ƙuri’unsu yadda ya kamata.
Ya ce jam’iyyarsa ba za ta amince da duk wani yunƙuri na maguɗin zaɓe ko karkatar da sakamakon zaɓe ba, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Ya kamata dukkanmu mu fito, mu kaɗa ƙuri’a sosai, mu kare ƙuri’unmu, sannan mu tabbatar an ƙirga su kuma an sanar da sakamakonsu.
“Ba za mu sake barin abin da ya faru a zaɓukan da suka gabata ya sake faruwa ba.”
Atiku ya yaba wa tarihin Sokoto
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana Sakkwato a matsayin muhimmiyar cibiyar siyasa da tarihi a Arewacin Najeriya da Yammacin Afirka.
Ya ce matsayin jihar a matsayin cibiyar Daular Usmaniyya ya sanya ta cikin muhimman wuraren tarihi a yankin.
Atiku ya kuma gode wa shugabannin ADC na jihar bisa shirya gangamin, inda ya yi zargin cewa jam’iyyar mai mulki a Sakkwato ta yi adawa da gudanar da taron.

Source: Facebook
An harbi magoya bayan ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ana zargin wasu jami’an rundunar Community Guards ta jihar Sokoto sun harbi mutane biyu da ake kyautata zaton magoya bayan jam’iyyar ADC ne a kan hanyar Sokoto zuwa Wurno.
An ce mutanen biyu da aka harba na cikin waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa wurin gangamin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng

