Yadda Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Abba a Kan Gawuna da APC a Zaben Kano

Yadda Kotun Koli Ta Tabbatar da Nasarar Abba a Kan Gawuna da APC a Zaben Kano

  • Alkalan kotun koli sun tabbatar da Abba Kabir Yusuf yana nan a kan kujerarsa
  • A hukuncin babban kotun kasar, an soke nasarar da kotunan baya suka ba APC
  • Kotun koli ta ce kuri’a ba ta haramta saboda rashin sa hannu da tambarin INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Wole Olanipekun SAN yake kare Abba Kabir Yusuf sai Nureni Jimoh SAN ya tsayawa APC a kotun koli a shari'ar zaben Kano.

John Okoro ya ce ana zargin Abba Kabir Yusuf da karyar zama ‘dan jam’iyya da kuma INEC da yin aringizon kuri’u a zaben da ya wuce.

Abba Kabir Yusuf
Kotun koli ta maida Abba Kabir Yusuf a mulki Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Hukuncin zaben Kano a kotun koli

Mai shari’a John Okoro ne ya karanto hukuncin da aka yi a kotun baya, kamar yadda Premium Times ta rahoto, ya gabatar da hukunci.

Kara karanta wannan

Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun koli ta ce saboda yawan ayyukan da ke gabanta, sai daga baya za a gabatar da dalilan da aka yi aiki da su wajen yanke hukunci.

1. NNPP ta maido kuri'u 165, 000

Mai shari'a John Okoro ya ci gyaran kotunan baya, ya tabbatarwa Abba Kabir Yusuf da NNPP kuri'u 165, 616 da aka soke masa a kotunan baya.

Kotun koli ta ce alkalai ba su da ikon amfani da dokar zabe wajen ruguza kuri’un da aka kada da sunan jam’iyyar NNPP a zaben gwamnan Kano.

Alkalan sun gamsu cewa babu abin da ke nuna ba daga wajen hukumar INEC kuri’un su ka fito ba, saboda haka aka yi watsi da duk karar APC.

A hukuncin kotun koli,kuri’a ba ta haramta saboda rashin sa hannu da tambarin INEC.

2. Abba 'dan jam'iyyar NNPP ne?

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta fara yanke hukunci kan shari’ar zaben gwamnan Kano

Okoro ya yi waje da hukuncin kotun daukaka kara da ta biyewa APC, ta ce Abba bai da shaidar zama ‘dan NNPP har ya shiga takara.

Alkalin ya ce APC ta dogara ne da cewa Abba Kabir Yusuf ba cikakken ‘dan NNPP ba ne.

Okoro ya shaida cewa babu ruwan kotu a wannan lokaci da gardamar zama ‘dan jam’iyya, ta ce wannan hurumin ‘yan jam’iyya ne ba ita ba.

A karshe babban kotun ta ce kotun sauraron korafin zabe ba ta haramtawa Abba Kabir Yusuf shiga takara ba, ta ce wannan shi ne daidai.

Hukuncin zaben Gwamnan Kano

An ji jotun koli ta tabbatar da nasarar NNPP a zaben gwamnan jihar Kano, ta karbi korafin Abba Kabir Yusuf da ya shiga a karshen 2023.

Hakan ya kawo karshen rigimar shugabanci da aka dauki watanni ana yi a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel