Abba Ya Yi Sauye Sauye a Gwamnatin Kano ban da Amincewa da Sababbin Kwamishinoni

Abba Ya Yi Sauye Sauye a Gwamnatin Kano ban da Amincewa da Sababbin Kwamishinoni

  • Abba Kabir Yusuf ya taba Majalisar zartarwarsa da duka kwamishinonin jihar Kano suke karkashinta
  • Gwamnan Kano ya dauke Abdullahi Waiya daga ma’aikatar labarai, ya maida shi ta matasa da wasanni
  • Akwai sababbin kwamishinonin da Abba ya rantsar, sun maye gurbin wadanda suka yi murabus a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Abba Kabir Yusuf ya canza wa wasu kwamishinoninsa ma’aikata da ya yi wa wasu sauye-sauye a jihar Kano.

Ban da nadin sababbin kwamishinoni da aka yi, Gwamnatin Kano ta sauya wa wasu daga cikinsu wuraren ayyukansu.

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf da kwamishinan ruwa a Kano Hoto: Dahiru M. Hashim
Source: Facebook

Abba Kabir ya sauya wasu kwamishinoni ma'aikata

Wani hadimin gwamnan, Abdullahi Ibrahim ya sanar da haka a dandalin X a yammacin Juma’a, 30 ga Oktoba 2026.

Abdullahi ya tabbatar da dauke Abdullahi Ibrahim Waiya daga ma’aikatar labarai zuwa ta harkar matasa da wasanni.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya maido Sheikh Masussuka Katsina ya fito da maganganu bayan rasuwa

Hamza Kachako da aka sani a ma’aikatar albarkatun kasa ya zama kwamishinan muhalli a gwamnatin Kano.

Dahiru Hashim zai rike kwamishinan ruwa

Shi Dahiru M. Hashim da yake kula da ma’aikatar muhalli zai cigaba da rike ma’aikatar ruwa matsayin cikakken kwamishina.

A shafin Facebook, Dr. Dahiru Hashim ya yi maganar rawar da ya taka wajen gyara muhalli da sauyin yanayi a kusan shekaru biyu.

Matashin ya ce a farkon Junairun 2025 gwamnan Kano ya ba shi wannan matsayi na kwamishina a majalisar zartarwa (SEC).

Dr. Hashim yana alfaharin yadda a yanzu ya ga an samu cigaba sosai a jihar, Kanawa suna tattuna abin da ya shafi muhallinsu.

A lokacin da ya yi a ofis, ya ce ya dasa miliyoyin bishiyoyi, sannan ya kawo wasu dokoki da za su yaki kazanta a jihar Kano.

Bayan haka an kawo sauyi a hukumar REMASAB wajen kwashe bola, kuma ana amfani da kazantar wajen zama taki a gonaki.

Hashim ya ce sun yi kokarin magance matsalolin zaizayar kasa, ambaliya tare da fito da kudirin rage dumamar yanayi a Kano.

Kara karanta wannan

Ziyarar Hannatu Musawa ofishin uban ‘ya ‘yanta, Abdussamad ya dawo da batun aure

A lokacinsa ne aka biya ma’aikata 2, 360 bashin albashin da suke bin gwamnatin jiha kuma aka kara wa masu shara albashinsu.

Sababbin kwamishinonin da aka nada a Kano

Da wannan canji da aka samu, jaridar Punch ta ce an bar ma’aikatun albarkatun kasa da na labarai babu kwamishinoni a jihar.

Dama can Air Commodore Salisu Yusha’u ya canji wani tsohon soja da irinsa da ya yi murabus, ya bar gwamnatin Abba Kabri.

Shi ma Ibrahim Namadi Dala da aka taba kora daga aiki saboda belin dillalin kwaya ya zama sabon kwamishinan kasuwanci.

Aminu Tsanyawa kuma ya hau kujerar kwamishina kimiyya da fasaha, Farfesa Sani Lawal M/fashi ya tafi ma’aikatar ilmi mai zurfi.

Muktar Ishaq Yakasai daga bangaren tsohuwar APC a Kano ya zama kwamishinan harkokin jin-kai da yaki da talauci na jihar.

Majalisa ta amince da zabin kwamishononin Abba

An ji labari dama Majalisar dokokin jihar Kano ta karɓi sunayen mutane shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura domin ya nada su.

Kara karanta wannan

Yadda Sheikh Yahaya Masussuka ya yi maganar mutuwa ana daf da harbe shi

Shugaban Majalisar, Jibril Ismail Falgore, ne ya karanta wasiƙar gwamnan da ya nemi a ba shi damar nada wasu a matsayin kwamishinoni.

A karshe dai an tantance mutanen shida da aka tura domin cikakken amincewa da su shiga majalisar zartarwa, su canji wadanda suka bar ofis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng