Gwamna Abba Ya Nada Sababbin Kwamishinoni, Mai Magana da Yawunsa Ya Samu Babban Mukami
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunayen Sanusi Bature Dawakin Tofa da Balarabe Sa’idu Gani ga Majalisar Dokokin Kano domin tantancewa
- Kakakin majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya ce za a gudanar da tantancewar ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, da ƙarfe 10 na safe
- Wannan na zuwa ne mako guda bayan majalisar ta tantance tare da amincewa da naɗin wasu mutane shida a matsayin kwamishinoni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zaɓi mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, domin naɗa shi a matsayin kwamishina a gwamnatin jihar.
Gwamnan ya kuma zaɓi Balarabe Sa’idu Gani domin muƙamin kwamishina, inda ya aika da sunayen mutanen biyu zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da amincewa da naɗinsu.

Source: Facebook
Kakakin majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar, bayan karanta wasiƙar da gwamnan ya aika domin neman amincewar ’yan majalisar kan naɗin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Yaushe za a tantance waɗanda aka zaɓa?
Falgore ya bayyana cewa za a gudanar da aikin tantance mutanen biyu ne a ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026, da ƙarfe 10:00 na safe.
Ya ce majalisar za ta gudanar da aikin bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, wanda ya tanadi rawar da majalisar za ta taka wajen tantance waɗanda gwamna ya zaɓa domin muƙaman kwamishinoni.
Sanusi Bature zai zama kwamishina
A halin yanzu, Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ne mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, sannan yana riƙe da muƙamin Darakta-Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a a Fadar Gwamnatin Kano.
Ya kasance ɗaya daga cikin manyan jami’an da ke isar da manufofi, ayyuka da shirye-shiryen gwamnatin Yusuf ga al’ummar jihar.
Idan majalisar ta amince da naɗinsa, hakan zai kawo ƙarshen aikinsa na yanzu a matsayin mai taimaka wa gwamna kan harkokin yaɗa labarai, inda zai koma cikin majalisar zartarwar gwamnatin jihar.
Abba ya aika da sunayen kwamishinoni 8
Sababbin sunayen da gwamnan ya aika wa majalisar sun zo ne kusan mako guda bayan ’yan majalisar sun tantance tare da amincewa da naɗin wasu mutane shida a matsayin kwamishinoni.
Daga cikin waɗanda aka amince da naɗinsu akwai tsohon kwamishina sau biyu, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa, da tsohon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, Farfesa Sani Lawan Malumfashi.
Wannan sabon mataki ya kai adadin waɗanda Gwamna Abba Yusuf ya miƙa sunayensu domin naɗa su kwamishinoni zuwa takwas, yayin da gwamnatinsa ke ci gaba da kammala tsarin kafa majalisar zartarwa.

Source: Facebook
Gwamna Abba ya yi sauye-sauye a gwamnatinsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aiwatar da wasu sauye-sauye a majalisar zartarwarsa.
Gwamna Abba ya dauke Abdullahi Ibrahim Waiya daga ma’aikatar labarai zuwa ta harkar matasa da wasanni.
Asali: Legit.ng

