Hadimin Tinubu Ya Fasa Kwai, Ya Tona Abin da Ya sa Kwankwaso Yake tare da Peter Obi

Hadimin Tinubu Ya Fasa Kwai, Ya Tona Abin da Ya sa Kwankwaso Yake tare da Peter Obi

  • Daniel Bwala ya yi zargin cewa Rabiu Kwankwaso ya marawa Peter Obi baya ne domin samun goyon bayan 'yan Kudu a 2031
  • Ya ce ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar bai ganin NDC za iya lashe zaben 2027, amma hadin kansu zai taimaka masa nan gaba
  • Bwala ya kuma zargi Obi da shiga takarar 2027 domin ci gaba da kasancewa a idon jama'a, ba wai don yana da tabbacin nasara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Daniel Bwala, Mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara a harkokin sadarwa da manufofi ya waiwayi alakar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Yana zargin cewa ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, yana tare da Peter Obi ne domin lissafin zaben shugaban kasa mai zuwa.

'Rabiu Kwankwaso yana hangen 2031 ne' - Daniel Bwala

Kara karanta wannan

'Arewa ta Tinubu ce': Fadar shugaban kasa ta fadi bangaren da Rarara ya yi fice

A hirarsa a tashar Channels, Daniel Bwala ya ce Rabiu Kwankwaso yana goyon bayan da zai taimake shi cimma burinsa na zama shugaban kasa ne.

Ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya yi amannar cewa Peter Obi ba zai ci zaben 2027 ba, amma yana fatan hadin kansu zai taimaka masa ya karbu a Kudu.

Idan ya iya samun karbuwa a sassan kasar nan, musamman a yankin Kudu inda Obi yake da karfi, Bwala ya ce wannan zai taimaki Kwankwaso a 2031.

A zaben shekarar 2031 ake sa ran mulki zai dawo yankin Arewa idan har Bola Tinubu ya zarce a badi.

Shi kuma Obi mai shekara 65 a duniya ya yi ikirarin cewa wannan ce takararsa ta karshe, ba zai sake neman mulki bayan zaben shekarar 2027 ba.

Ya ce:

"Kwankwaso, ina da dalilin yarda cewa ya shiga tafiyar Obi ne saboda burinsa na 2031. Ya san cewa Obi ba zai yi nasara ba, amma yana bukatar samun karbuwa a wurare daban-daban."

Ya kara da cewa:

"Idan lokacin takararsa ya zo, 'yan Kudu za su ce, 'Ai ya goyi bayan Peter Obi namu, bari mu ma mu goya masa baya.' Ya san cewa Obi ba zai kai ga samun nasara ba."

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Mutumin Kwankwaso, Dantiye ya fadi wanda zai zaba a Kano

Daniel Bwala ya raina takarar Peter Obi

The Cable ta ce a hirar tasu, ya yi watsi da tasirin Obi a zaben shugaban kasa na 2027, yana mai jaddada cewa Tinubu zai doke abokan hamayyarsa.

Bwala ya kuma ce Obi ya shiga takarar ne musamman domin ci gaba da kasancewa cikin labaran da ake yadawa a kafafen yada labarai na zamani.

Hadimin shugaban na Najeriya ya raina burin ‘dan takaran na jam’iyyar NDC duk da cewa ya tashi da kuri’u sama da miliyan shida da ya nemi mulki a LP.

A ra’ayin kwararren lauyan, Obi bai hango nasara illa dai kamar yana shirin wasan kwaikwayo ne.

Tsohoun gwamnan na jihar Anambra ya samu karbuwa sosai musamman a yankin Ibo inda ya samu kusan 90% na kuri’un jihohinsu a zaben 2023.

Dan Bello suna tare da Seyi Tinubu?

Labari ya zo cewa ana barazanar kashe Abdul Turaki tun da ya fito ya zargi Dan Bello da aiki da su Seyi Tinubu a boye domin gwamnatin APC ta zarce.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya hada Kwankwaso da Obi ya yi masu rubdugu kan 2027

Mista Abdul Turaki yana ganin ta kan shi domin ana barazanar hallaka shi, saboda haka ne kungiyar Amnesty International ta ce dole a ba shi kariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng