Obi na Zargin ana Shirin Alakanta Shi da 'Yan Ta'adda don Bata Shi a Arewa

Obi na Zargin ana Shirin Alakanta Shi da 'Yan Ta'adda don Bata Shi a Arewa

  • Ofishin yada labaran Peter Obi ya yi gargadi kan wani zargin shirin farfaganda da ake yi domin alakanta tsohon gwamnan da kungiyar IPOB
  • Ya ce wasu ’yan jam’iyyar mai mulki da wasu ’yan adawa na kokarin amfani da batun domin hana ’yan Arewa goyon bayan hadakar siyasar Obi da Kwankwaso
  • Obi ya bukaci kafafen yada labarai su tabbatar da sahihancin duk wani rahoton siyasa kafin wallafa shi, musamman wanda zai iya haifar da rabuwar kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ofishin yada labaran Peter Obi ya yi zargin cewa wasu ’yan jam’iyya mai mulki da wasu daga cikin ’yan adawa na shirin kulla wata makarkashiya domin alakanta shi da kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a madadin Peter Obi, Idris Zekeri Jnr., ya ce bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa ana shirin kaddamar da kamfen din bata suna.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun tarwatsa layin wutar lantarki a Najeriya

Peter Obi
Dan takarar NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa za a masu haka ne domin amfani da bambancin kabila da matsalar tsaro wajen nisantar da ’yan Arewa daga Obi da hadakarsa da Rabiu Kwankwaso.

Batun bata sunan Obi a Arewa

Sanarwar ta ce ana sa ran wadanda ke da hannu a shirin za su yi amfani da jaridun Arewa, gidajen rediyo da kuma kafafen sada zumunta wajen yada ikirarin cewa Obi na da alaka da masu fafutukar ballewar Biafra da kuma shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.

A matsayin misali, ofishin ya ambaci wani mai amfani da kafafen sada zumunta mai suna Gucci Commando, wanda ya yi ikirarin cewa ya ziyarci Nnamdi Kanu a Sokoto tare da danganta shi da goyon bayan takarar Obi.

Sai dai ofishin yada labaran Obi ya yi watsi da ikirarin, yana mai cewa babu wata sahihiyar hujja da ta tabbatar da shi.

Kara karanta wannan

An gwabza rikici tsakanin sojoji da jama'a a Lawanti da ke Gombe

Obi ya wanke kan shi

Ofishin ya jaddada cewa Peter Obi ba dan takarar wata kabila ko addini ba ne, illa dan Najeriya da manufofinsa suka shafi dukkan yankuna da al'ummomin kasar.

Ya ce goyon bayan Obi ga adalci, tattaunawa, sulhu tsakanin al'umma da bin doka da oda bai kamata a fassara shi a matsayin goyon bayan ballewa ko raba Najeriya ba.

Peter Obi da Rabiu Kwankwaso
Dan takarar NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso. Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa sanarwar ta kara da cewa hadakar siyasar Obi da Kwankwaso wani yunkuri ne na kasa baki daya, ba wani shiri na wata kabila ba.

Maganar kudin kamfen din NDC

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar NDC ta yi magana kan rahotannin cewa akwai sabani tsakaninta da Peter Obi kan yadda za a sarrafa kudin yakin neman zabensa.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben, Constance Ikokwu, ta bayyana rahotannin sabanin da ake zargin ya shiga tsakanin jam’iyyar da dan takararta a matsayin labarin karya.

Karyatawar ta zo ne bayan takaddama kan yadda za a gudanar da gudummawar kudin yakin neman zaben Obi, biyo bayan shirin tara kudi da Aisha Yesufu ta kaddamar domin tallafa wa takararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng