2027: Sarkin Musulmi Ya Gana da Atiku da Manyan ADC a Sokoto

2027: Sarkin Musulmi Ya Gana da Atiku da Manyan ADC a Sokoto

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna
  • Sarkin ya yi kiran ne lokacin da ya karɓi tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya kai masa ziyarar girmamawa a fadarsa da ke Sokoto
  • Atiku ya gode wa Sarkin Musulmi bisa kyakkyawar tarbar da ya yi masa, tare da jaddada muhimmancin rawar sarakunan gargajiya wajen tabbatar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Sokoto – Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci 'yan Najeriya da su haɗa kai domin magance ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Laraba lokacin da ya karɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tare da tawagarsa a fadarsa da ke Sokoto.

Kara karanta wannan

Mutanen Tinubu sun fita daga APC sun koma wajen Atiku a ADC

Sarkin Musulmi Atiku da su Abubakar
Sultan tare da manyan ADC a jihar Sokoto. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Source: Facebook

Maganar Sultan kan zaman lafiya

A sakon da ya wallafa a Facebook, Sarkin Musulmi ya bayyana cewa zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna su ne ginshiƙan magance matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Ya kuma jaddada cewa kowa na da rawar da zai taka wajen gina ƙasa, yana mai cewa sarakunan gargajiya na da muhimmiyar gudunmawa wajen tabbatar da zaman tare da ci gaba mai ɗorewa.

A kalamansa:

"Zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna suna da matuƙar muhimmanci wajen magance ƙalubalen da ƙasarmu ke fuskanta. Dole ne kowa ya ɗauki nauyin da ke kansa wajen gina al'umma mafi kyau."

Atiku ya gode wa Sultan

A nasa jawabin, Atiku Abubakar ya gode wa Sarkin Musulmi bisa kyakkyawar tarba da karamcin da ya nuna masa da tawagarsa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya amince da muhimmiyar gudunmawar da sarakunan gargajiya ke bayarwa, musamman Sarkin Musulmi, wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yaba wa Sarkin Musulmi a bikin cika shekara 20 a mulki

Atiku ya ce:

"Muna godiya ga Mai Martaba bisa kyakkyawar tarbar da ya yi mana. Sarakunan gargajiya suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa."

Punch ta wallafa cewa ya kuma jaddada buƙatar haɗin kan al'umma domin gina Najeriya mai inganci da wadata.

Ziyarar ta ba Atiku da Sarkin Musulmi damar tattauna batutuwan da suka shafi ƙasa, musamman yadda za a ci gaba da inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.

Atiku Abubakar da 'yan Tinubu Must Go
Atiku Abubakar tare da su Abba Hikima 'yan Tinubu Must Go. Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

Sarkin Musulmi ya samu rakiyar Wazirin Sokoto, Magajin Rafin Sokoto, Galadiman Garin Sokoto, Sa'in Kilgori da Sakataren Majalisar Masarautar Sokoto.

Sultan ya karrama Bala Lau

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya karrama shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

An bai wa malamin lambar yabo mai suna “Sheikh Abdullahi Fodiyo Exemplary Prize for Knowledge and Scholarship” ta shekarar 1448AH/2026.

An karrama Sheikh Bala Lau ne bisa gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimin Musulunci da yaɗa koyarwar Sunnah ta Annabi Muhammad (SAW).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng