Awanni 24 Bayan Bikin Cika Shekaru 56, Allah Ya Yi wa Ssnatar APC Rasuwa
- Sanata mai wakiltar Lagos ta Yamma, kuma tsohuwar mataimakiyar gwamnan Jihar Lagos, Dakta Idiat Adebule, ta rasu
- Ta rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke GRA, Ikeja, kwanaki kaɗan bayan ta yi bikin cika shekaru 56
- Jam’iyyar APC ta ɗage gangamin yaƙin neman zaɓen sanatan da aka shirya gudanarwa ranar Litinin, 30 ga Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Sanata mai wakiltar mazabar Lagos ta Yamma, kuma tsohuwar mataimakiyar gwamnan Jihar Lagos, Dakta Idiat Adebule, ta rasu.
Rahotanni sun ce an tabbatar da rasuwarta ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke unguwar GRA, Ikeja, a Jihar Lagos.

Source: Facebook
Wani majiya da ke kusa da marigayiyar ya tabbatar wa jaridar Daily Trust rasuwarta, amma bai bayyana musabbabin mutuwar ba.
Adebule, wadda ke neman sake zaɓenta domin wa’adi na biyu a Majalisar Dattawa, ta rasu ne sa’o’i ƙasa da 24 bayan bikin cikarta shekaru 56 a duniya.

Kara karanta wannan
Sanata ya yi magana kan saƙon 'yan sanda bayan an yi yunƙurin kashe shi a wurin kamfe
An samu labarin cewa likitocin asibitin ne suka tabbatar da rasuwarta a daidai lokacin da mambobin mazabarta ke shirye-shiryen gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen Sanatan Lagos ta Yamma, wanda aka tsara gudanarwa ranar Litinin, 30 ga Nuwamba, 2026.
An shirya gudanar da gangamin ne a Kwalejin ’Yan Sanda da ke GRA, Ikeja, da ƙarfe 11 na safe, amma yanzu kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan Jihar Lagos na jam’iyyar APC ya ɗage taron.
A cikin sanarwar ɗage taron, kwamitin ya ce zai sanar da sabuwar ranar gudanar da gangamin nan gaba, tare da ba da haƙuri kan duk wata matsala da matakin zai iya jawo wa jama’a.
Mai magana da yawun APC a Lagos, Mogaji (Hon.) Seye Oladejo, ne ya sanya hannu kan sanarwar.
Ta yi bikin cika shekaru 56
Sanatar, wadda ta cika shekaru 56 a ranar Juma’a, ta wallafa saƙon murnar zagayowar ranar haihuwarta a shafinta na X.
Ta rubuta cewa:
“Yau, na mayar da dukkan godiya da yabo ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa rahamarsa marar iyaka, ni’imarsa da kuma baiwar rayuwa, yayin da nake bikin ƙarin shekara guda a rayuwata.
“Ina matuƙar godiya gare Shi bisa shiriyarsa, kariyarsa da kuma dimbin ni’imomin da Ya yi mini. Addu’ata ita ce wannan sabon shekaru ya zo mini da ƙarin kuzari domin ci gaba da yi wa al’umma hidima da bayar da gudummawa mai ma’ana ga bunƙasa da ci gaban Lagos ta Yamma, Jihar Lagos da kuma ƙasarmu ƙaunatacciya. Alhamdulillah bisa ƙarin shekara guda!”
Asali: Legit.ng