Gwamnatin Tinubu Ta Kwantar da Hankulan Yan Najeriya, Ta Dauki Alkawari kan Zaben 2027
- Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin Tinubu za ta samar da isasshen tsaro a zaɓen 2027
- Ya ce jami’an tsaro za su kare masu zaɓe, ma’aikatan zaɓe da sauran jama’a kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan kammala shi
- Ribadu ya yi kira ga ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa su guji tashin hankali tare da mutunta ’yancin sauran jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta samar da tsaron da ake buƙata domin gudanar da babban zaɓen 2027 cikin lumana, gaskiya da sahihanci.
Ribadu ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja, yayin taro kan tsaron zaɓe gabanin babban zaɓen 2027, wanda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shirya.

Kara karanta wannan
"Dan takarar haɗakar adawa zai iya kayar da Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027"

Source: Twitter
Ya ce gwamnatin tarayya ta himmatu wajen tabbatar da gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.
Alkawurran gwamnatin Tinubu kan zabe
Nuhu Ribadu ya ce:
“Gwamnatin Shugaba Tinubu, wanda shi mai kishin dimokuraɗiyya ne, ta himmatu wajen samar da tsaron da ake buƙata domin gudanar da zaɓe cikin lumana, gaskiya da sahihanci. Babu shakka a kan hakan.”
Ya bayyana cewa aikin gwamnati da hukumomin tsaro shi ne kare masu zaɓe, jami’an gudanar da zaɓe da sauran al’umma kafin zaɓe, lokacin zaɓe da kuma bayan an kammala.
“Ya zuwa yanzu, ina ganin mun yi abin a yaba a ƙarƙashin wannan gwamnati idan aka kwatanta da abubuwan da muka gani a baya.
"Muna kare ku, muna kare masu zaɓe, muna kare ’yan siyasa. Ko bayan zaɓe ma, muna tabbatar da cewa ba a samu tashin hankali ba," in ji shi.
Ribadu ya yi magana kan yancin INEC

Kara karanta wannan
Nuhu Ribadu ya gano yadda ake amfani da kafafon sada zumunta a haddasa rikici a Najeriya
Ribadu ya ce dole ne a kare tare da mutunta ’yancin da kundin tsarin mulki ya bai wa INEC, musamman ganin cewa farfesa a fannin shari’a ne ke jagorantar hukumar.
Ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su gudanar da ayyukansu ba tare da nuna bambanci ba, kuma bisa tanadin doka.
Ya yaba wa kwamishinonin INEC, masu ruwa da tsaki da kafafen yaɗa labarai, yana mai cewa yadda ake gudanar da zaɓe a Najeriya na samun ci gaba da inganta.
Ya aika sako ga ’yan siyasa
Da yake magana kan sahihancin zaɓe, Ribadu ya ce gaskiya da riƙon amana suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da amincewar jama’a ga sakamakon zaɓe.
Ya ce dukkan ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki suna da alhakin yin watsi da tashin hankali, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

Source: Facebook
Ya ce:
“Dimokuraɗiyya na buƙatar mutunta ra’ayoyi daban-daban, ’yancin shiga harkokin siyasa da kuma ɗabi’a mai kyau. Dukkan ’yan siyasa suna da alhakin ƙin amincewa da tashin hankali da kuma mutunta haƙƙin sauran mutane.”
Ribadu ya yi gargadin cewa rikice-rikicen da suka faru a baya-bayan nan da suka shafi zaɓe sun nuna muhimmancin yin shiri tun da wuri da kuma ɗaukar matakan kariya.

Kara karanta wannan
"Shugaba Tinubu ya kunyata 'yan adawa, ya nuna ƙarfin da yake da shi a Arewacin Najeriya"
Ribadu ya gano illar kafar sada zumunta
Kun ji cewa Nuhu Ribadu ya bayyana cewa ana amfani da kafofin sada zumunta wajen yaɗa labaran ƙarya da tayar da rikici tsakanin al’umma a Najeriya.
Ya bayyana cewa ƙaruwar tasirin kafofin sada zumunta da fasahar AI sun sauƙaƙa wa mutane yaɗa bayanan ƙarya da za su iya haddasa zaman doya da manja tsakanin al’ummomi.
Asali: Legit.ng