Har An Fara Samun Masu Meman Su Gaji Tinubu a Aso Rock cikin ‘Yan Jam’iyyar APC
- Jam’iyyar APC a shiyyar Arewa ta Tsakiya ta nemi a ba yankin damar samar da shugaban Najeriya a shekarar 2031
- Shugaban ƙungiyar, Saleh Zazzaga, ya ce za su taimaka wa Bola Tinubu ya samu aƙalla 80% na ƙuri’unsu a zaɓen 2027
- Ya ce goyon bayan Tinubu zai taimaka wajen tabbatar da burinsu na karɓar shugabancin ƙasa a karon farko a tarihin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ƙungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta fara nuna sha’awar samun shugabancin Najeriya a 2031, ta kuma nuna tana tare da Bola Tinubu.
APC ta Arewa ta Tsakiya ta nemi a ba yankin damar samar da shugaban Najeriya a shekarar 2031, tare da alƙawarin ba APC ƙuri’un yankin a 2027.

Source: Twitter
Ana shiga lissafin samun mulkin Najeriya a 2031
A rahoton The Nation aka fahimci APC a yankin yana harin ba Shugaba Bola Tinubu aƙalla kashi 80 cikin 100 na ƙuri’un mutanen ta don a zarce.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: An huro wa Atiku wuta kan neman takarar shugaban ƙasa a zaben 2027
Ƙungiyar ta ce goyon bayan da take ba wa Tinubu ya samo asali ne daga tsammanin shugabancin zai koma Arewa bayan an kammala wa’adin nan.
‘Yan jam’iyyar sun kuma dage cewa ya kamata a ba Arewa ta Tsakiya damar yin mulki a Najeriya.
"Shekarar 2031 ita ce shekarar da ya kamata mu samar da shugaban Najeriya. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa al'ummar Arewa ta Tsakiya suka yanke shawarar zaɓen Shugaba Bola Tinubu da ƙuri'u masu yawa a zaɓen 2027.
'Yan APC na Arewa ta tsakiya sun yi taro
Shugaban ƙungiyar, Saleh Zazzaga, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Abuja, yayin da yake sanar da matsayar da suka cimma a wani taron su.
Masu ruwa da tsaki na ƙungiyar daga jihohin Filato, Benuwai, Nasarawa, Neja, Kogi da Kwara sun yi zamansu na ƙarshen shekara a birnin tarayya.
Mista Saleh Zazzaga ya ce yankin na da haƙƙin neman shugabancin ƙasa, kasancewar har yanzu bai taɓa samar da shugaban ƙasa ko mataimakinsa ba.

Kara karanta wannan
"Shugaba Tinubu ya kunyata 'yan adawa, ya nuna ƙarfin da yake da shi a Arewacin Najeriya"
Ya bayyana wannan a matsayin rashin adalci, yana mai cewa ya kamata a yi la'akari da daidaito da adalci wajen rabon shugabancin ƙasa tsakanin shiyyoyi.
Za a ba Tinubu 89% na kuri'un yankin
Zazzaga, wanda ‘dan kwamitin yaƙin zaɓen shugaban ƙasa ta APC ne, ya ce masu ruwa da tsakin sun amince su yi aiki domin ganin nasarar Tinubu.
Yake cewa za su tabbatar da cewa Arewa ta Tsakiya ta samu matsayi mai kyau a tsarin rabon mukamai, labarin ya zo a jaridar Punch ranar Asabar.
Domin nuna da gaske suke yi, Zazzaga ya ce:
"Mun yanke shawarar cewa ba za mu bari wani daga Arewa ta Tsakiya ya goyi bayan wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ba daga yankin yake ba."
‘Dan siyasar ya ce sam ba a ganin tasirin manyan jam'iyyun adawa na ADC da NDC a Arewa maso tsakiya.
"Idan ka duba Arewa ta Tsakiya, za ka lura cewa manyan jam'iyyun adawa, ADC da NDC, ba sa gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.
"Hakan ya faru ne saboda al'ummar yankin sun yanke shawarar zaɓen Tinubu da ƙuri'u masu yawa a zaɓe mai zuwa, domin kada wani ya yi takara da mu a 2031."
- Saleh Zazzaga

Source: Twitter
Abba Hikima yana da ja da shiga APC
A nan aka ji cewa Abba Hikima Fagge ya ba abokan gwagwarmayarsa shawara lokacin da irinsu Bulama Bukarti suka yi tsalle suka shiga APC.
Lauyan ya yi magana yana cewa bai ganin kuskuren ’yan gwagwarmaya idan sun shiga harkokin siyasa, amma kyau su tafi wata jam’iyyar adawa.
Ɗan gwagwarmayar ya bayyana rawar da masu fafutukar neman sauyi ke iya takawa wajen ƙalubalantar gwamnati da neman sauyi a siyasa.
Asali: Legit.ng
