Ministan Tinubu Ya Fito Ya Yi Maganganu kan Rusa Takarar Atiku

Ministan Tinubu Ya Fito Ya Yi Maganganu kan Rusa Takarar Atiku

  • Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya yi maraba da hukuncin kotu da ya rusa shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark
  • Keyamo ya ce ƙungiyar haɗakar da ta karɓi ragamar jam’iyyar ba ta samu izinin hukumomin ADC ba kafin ta gudanar da sauye-sauyen shugabanci
  • A nasa martanin, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da kotu da wasu dabaru domin kawo cikasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ministan Sufurin Jiragen Festus Keyamo, ya nuna goyon bayansa ga hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta rusa shugabancin jam’iyyar ADC ƙarƙashin Sanata David Mark.

Kotun ta soke matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Obi ya shiga wa Atiku fada kan rusa 'yan takarar ADC da kotu ta yi

Festus Keyamo da Atiku Abubakar
Festus Keyamo a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Festus Keyamo|Atiku Abubakar
Source: Twitter

The Sun ta wallafa cewa Keyamo ya bayyana cewa ƙungiyar haɗakar da ta karɓi ragamar ADC ta yi hakan ne ba tare da izinin hukumomin jam’iyyar ba.

Bayanin da Keyamo ya yi

Ministan ya ce ba daidai ba ne wasu mutane su karɓi ikon jam’iyyar siyasa da ’yan Najeriya suka kafa ba tare da bin ƙa’idojin kundin tsarin mulkinta ba.

A cewarsa, bai kamata wani mutum da ke ikirarin shugabantar jam’iyya ya taimaka wa wasu su karɓi ragamar ta ba tare da gudanar da taron kwamitin zartarwa na ƙasa ko ƙaramin babban taron jam’iyya da amincewarsu ba.

Keyamo ya kuma zargi ƙungiyar da David Mark ke jagoranta da ƙoƙarin ɗaura wa jam’iyyar APC alhakin matsalar da ta shiga.

Ya dage cewa kotun ta yanke hukuncin ne bisa hujjojin da aka gabatar mata, ba wai saboda matsin lamba ko ra’ayin wasu mutane ba.

Sowore ya zargi Tinubu da karfa-karfa

A nasa martanin, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarAAC, Omoyele Sowore, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da shari’a a matsayin dabarar kawo cikas ga ’yan Najeriya masu shirin kalubalantarsa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Ko a jiki na," Atiku ya maida martani bayan kotu ta rushe takararsa a zaben 2027

Sowore ya ce shari’o’in da ake yi wa jam’iyyun siyasa, musamman ADC, na daga cikin dabarun da ya yi zargin Tinubu ke amfani da su domin rikitar da ’yan Najeriya da hana su tsayawa takara.

Omoyele Sowore
Dan takarar AAC, Omoyele Sowore. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, ya yi zargin cewa ana amfani da kotuna ta hanyar wasu ’yan siyasa, yayin da a wasu lokuta ake amfani da tashin hankali wajen hana ’yan adawa gudanar da harkokinsu.

Sowore ya yi kira da a tunkari irin waɗannan dabaru ta hanyar abin da ya kira gwagwarmayar juyin-juya-hali, yana mai cewa dabarun da ake zargin ana amfani da su ba za su hana sauyin siyasa ba.

Nafiu Bala ya yi murna

A wani labarin, mun ruwaito cewa Nafiu Bala, wanda ke ikirarin shi ne sahihin shugaban jam’iyyar ADC, ya yi murnar hukuncin kotu da ya soke shugabancin Sanata David Mark.

Hukuncin kotun ya kuma rusa matakan da shugabancin Mark ya ɗauka, lamarin da ka iya shafar takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a jam’iyyar.

Sai dai wasu jiga-jigan ADC da magoya bayan Atiku sun yi martani daban-daban kan hukuncin, inda wasu suka nuna rashin amincewa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng