Sabuwar Rigima Ta Barke kan Atiku Ya Kira Tinubu da Sunan da 'bai Dace ba'
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya caccaki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar kan kiran Shugaba Bola Tinubu da sunansa na asali
- Keyamo ya bayyana kiran Shugaban Ƙasar da “Bola” a matsayin rashin ladabi da girmamawa, yana mai cewa mukamin shugaban ƙasa ya cancanci mutuntawa
- Martanin Keyamo ya biyo bayan wata sanarwa da Atiku ya yi a Abuja, inda ya buƙaci Tinubu ya amince da shawararsa kan rage farashin man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya mayar da martani ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, kan yadda yake kiran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da “Bola”.
Hakan na zuwa ne bayan Atiku ya yi kira ga shugaban Najeriya da ya rage tsadar man fetur a wani taron menema labarai a Abuja.

Source: Facebook
Keyamo ya yi martani ga Atiku ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, inda ya ce irin wannan kiran bai dace da matsayin Shugaban Ƙasa ba.
Tinubu: Zargin Keyamo ga Atiku
Festus Keyamo ya ce ci gaba da kiran Shugaba Tinubu da sunansa na asali abu ne da ke nuna rashin ladabi da girmamawa.
Ya ce ko da yake akwai bambancin ra’ayi tsakanin ‘yan siyasa, ya kamata a girmama matsayin shugaban ƙasa saboda mutuncin ƙasar.
Ya ce:
“Ci gaba da kiran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ‘Bola’ da Mai Girma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya yi a taron manema labaransa na yau rashin ladabi da girmamawa ne ƙwarai.
“Ya kamata ya sani cewa ko da wane irin bambanci yake tsakaninsa da Shugaban Ƙasa, saboda ƙasar nan, ya kamata a bai wa wannan mukami dukkan mutuncin da ya dace da shi.”

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC
Batun shekarun Bola Tinubu
Ministan ya kuma danganta kalaman Atiku da wata magana da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi a baya kan shekarun Tinubu.
Keyamo ya ce Atiku ya yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu ya fi shi shekaru, don haka ya ce akwai saɓani a kiran wanda ya bayyana a matsayin “dattijo” da sunansa na asali.

Source: Facebook
Ya kuma zargi Atiku da yin magana ne bisa wani abu da ya shafi kansa, yana mai cewa yanayin maganarsa na nuna takaici da ɗaci..
Martanin Atiku ga APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya ce kotun sasanta rikicin kasuwanci ta ICC da ke Paris ba ta yanke wani hukunci da ya same shi da laifin cin hanci da rashawa kan batun aikin wutar Mambilla ba.
Atiku ya bayyana cewa bai kasance cikin kwamitin da ya bayar da kwangilar aikin ga Sunrise Power ba, yayin da martaninsa ya biyo bayan matsayar kwamitin yaƙin neman zaɓen APC kan wata dala 500,000 da aka tura wa tsohuwar matarsa.
Batun ya sake kunno kai ne bayan APC ta buƙaci Atiku ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027, tana zargin cewa abin da ya faru kan kuɗin ya jefa ayar tambaya kan rawar da ya taka a aikin Mambilla.
Asali: Legit.ng
