Jirgin Sojoji Ya Yi Hadari a Yankin da 'Yan Tawaye ke Zama, Dakaru Sun Rasu
- Aƙalla jami’an sojin Peru takwas sun mutu bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojin ƙasar ya yi haɗari a wani yanki mai nisa
- Jirgin ya yi haɗarin ne kusa da garin Sanabamba yayin wani aikin ceto sojoji a kwarin kogunan Apurimac, Ene da Mantaro
- Matukin jirgin ne kaɗai ya tsira daga cikin mutum tara da ke cikinsa, kuma an garzaya da shi zuwa babban birnin ƙasar domin samun kulawar likitoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Peru – Jami’an sojin Peru takwas sun mutu bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojin ƙasar ya yi haɗari a wani yanki da ake zargin ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi da ragowar ’yan tawayen Shining Path suna gudanar da ayyukansu.
Ma’aikatar tsaron ƙasar ta tabbatar da mutuwar jami’an, inda ta ce matukin jirgin ne kaɗai ya tsira daga cikin mutum tara da ke cikinsa.

Source: Getty Images
BBC ta ruwaito cewa jirgin ya yi haɗarin ne kusa da garin Sanabamba yayin wani aikin kwashe jami’an sojin ƙasa da ke cikin kwarin kogunan Apurimac, Ene da Mantaro, wanda aka fi sani da VRAEM.
Yadda jirgin ya yi haɗari
Rahoton A News ya nuna cewa ma’aikatar tsaron Peru ta ce jirgin ya ɓace ne a daren Alhamis bayan ya kammala aikin ceto wasu jami’an sojin ƙasa uku.
Sai dai ba a bayyana dalilin da ya sa sojojin suke buƙatar ceto ba, amma daga baya aka tabbatar cewa suna cikin waɗanda suka mutu a haɗarin.
Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatar ta ce jami’an bincike da ceto sun gano jirgin tare da jami’an soji tara da ke cikinsa.
Ta bayyana sunan matukin jirgin a matsayin Enzo Espinoza Roque, wanda aka kwashe zuwa birnin Lima domin samun kulawar likitoci ta musamman.
Yankin da jirgin ya yi hadari
Wasu rahotanni da aka tabbatar sun nuna cewa jirgin ya faɗo ne a yankin VRAEM, wanda aka fi sani da kwarin hodar iblis.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun tarfa mutanen gari da daddare, sun kashe mata, yara da matasa da dama
Yankin shi ne mafi girman wurin noman ganyen coca a Peru, wanda ake sarrafawa wajen samar da hodar iblis.
Haka kuma, ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi da ragowar ƙungiyar ’yan tawayen Shining Path suna gudanar da ayyukansu a yankin.
Peru na daga cikin manyan ƙasashen duniya da ke samar da ganyen coca da hodar iblis, tare da Colombia, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.

Source: Getty Images
Babban kwamandan rundunar sojin Peru ya wallafa saƙon ta’aziyya a intanet, inda ya miƙa saƙon jaje ga iyalan jami’an da suka rasu, abokansu da sauran abokan aikinsu.
Jirgi ya yi hadari a Amurka
A wani labarin, kun ji cewa mutane shida, ciki har da yara maza biyu masu shekaru 8 da 10, sun mutu bayan wani ƙaramin jirgin sama ya faɗa cikin teku a Amurka.
Jirgin samfurin Cessna 210 ya tashi ne daga birnin New Orleans zuwa Fort Myers da ke jihar Florida kafin ya faɗa cikin Tekun Mexico.
Jami’an tsaron gabar teku na Amurka sun ce an gano gawarwakin mutum shida a cikin jirgin bayan shafe sa’o’i ana gudanar da aikin ceto.
Asali: Legit.ng
