Faransa Ta Tsunduma Yanayin Koma Bayan Tattalin Arziki

Faransa Ta Tsunduma Yanayin Koma Bayan Tattalin Arziki

  • Tattalin arzikin Faransa ya shiga koma bayan sababbin alkaluma sun nuna cewa ya samu raguwar ci gaba fiye da yadda aka yi hasashe a baya
  • Hukumar S&P ta sauya hasashen darajar bashin ƙasar daga matsakaici zuwa mara kyau, sakamakon ƙaruwar matsin tattalin arziki da tsadar biyan ruwa kan basussuka
  • Gwamnatin Faransa na fuskantar ƙalubalen rage gibin kasafin kuɗi zuwa 5% na tattalin arzikin ƙasar a shekarar 2027, yayin da zaɓen shugaban ƙasa ke gabatowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Paris, Faransa – Tattalin arzikin Faransa ya shiga koma bayan tattalin arziki a hukumance bayan alkaluman da aka fitar sun nuna cewa tattalin arzikin ƙasar ya samu koma baya a zangon wata uku na shekarar 2026.

Rahoto ya nuna cewa raguwar tattalin arzikin ta jefa burin gwamnatin ƙasar na samun ci gaban tattalin arziki da 0.5% a wannan shekarar cikin barazanar rashin cimmawa.

Kara karanta wannan

Ina N450bn ta shiga? Atiku ya ɗauko magana mai girma kan tallafin manoma a Najeriya

Emmanuel Macron
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar The Independent ta ruwaito cewa lamarin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin ƙasar ke ƙoƙarin rage gibin kasafin kuɗi da kuma shawo kan matsin tattalin arziki.

S&P ta sauya hasashe kan Faransa

Hukumar tantance darajar bashin ƙasashe ta S&P ta sauya hasashen darajar bashin Faransa daga matsayin da ya nuna yana daidai zuwa cikin hadari a ranar Juma'a.

Sai dai hukumar ta bar darajar bashin ƙasar a matakin A+/A-1, tana mai bayyana damuwarta kan yadda ƙarancin ci gaban tattalin arziki da ƙarin kuɗin ruwa kan basussuka ke kawo cikas ga rage gibin kasafin kuɗi.

S&P ta kuma yi hasashen cewa gibin kasafin kuɗin Faransa a shekarar 2026 da 2027 zai fi wanda ta yi hasashe a baya.

Hukumar ta ce rarrabuwar kawuna a siyasar ƙasar na iya ci gaba da kawo cikas ga aiwatar da matakan rage kashe kuɗi da gyare-gyaren da za su inganta tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya gano yadda ake amfani da kafafon sada zumunta a haddasa rikici a Najeriya

Faransa na fama da bashi

Rahoton ya nuna cewa kuɗin ruwa kan bashin gwamnatin Faransa na shekaru 10 ya haura 5.14% a watan da ya gabata, matakin da ba a gani ba tun shekarar 2002.

Wannan ya faru ne sakamakon fargabar masu zuba jari kan yadda ƙasar za ta iya rage gibin kasafin kuɗi, tabbatar da amincewa da kasafin kuɗin 2027 da kuma shawo kan matsalolin zamantakewa da tsadar rayuwa ke haifarwa.

Reuters ta wallafa cewa gwamnatin ƙasar mai rinjayen marasa rinjaye na ƙoƙarin samun amincewar majalisar dokoki kan kasafin kuɗin shekarar 2027.

Emmanuel Macron
Shugaba Emmanuel Macron na magana da waya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kasafin na da burin rage gibin kuɗi daga 5.4% na tattalin arzikin ƙasar a shekarar 2026 zuwa 5% a shekarar 2027.

An yi guguwa a Amurka

A wani labarin, kun ji cewa wata guguwa dauke da ruwan sama mai karfi ta haddasa katsewar wutar lantarki ga gidaje da wuraren kasuwanci kusan miliyan daya a Amurka.

An kuma samu cikas a zirga-zirgar jiragen sama, inda aka jinkirta tashin sama da jirage 2,000 tare da soke wasu fiye da 400 a birane da dama.

Rahoto ya nuna cewa guguwar ta kuma tilasta dage bikin faretin ranar godiya ta Thanksgiving da ake gudanarwa duk shekara a birnin New York

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng