Sanata Dino Melaye Ya Jagoranci Yi Wa Tinubu 'Allah Ya Isa' Kafa 3 a Gangamin ADC
- Sanata Dino Melaye ya jagoranci magoya bayan ADC wajen furta kalmar “Allah Ya Isa” ga Shugaba Bola Tinubu bayan hukuncin babbar kotu tarayya
- Babbar kotun ta russ tsagin ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark, wanda hakan ya soke takarar Atiku Abubakar a zaben 2027
- Dino Melaye ya kwatanta kudaden da aka kashe a karkashin Buhari da na gwamnatin Tinubu kan Service-Wide Votes
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kebbi, Nigeria - Sanata Dino Melaye ya jagoranci magoya bayan jam’iyyar ADC wajen furta “Allah Ya Isa” kafa uku kamar yadda ya fada ga Shugaba Bola Tinubu.
Melaye, wanda ke rike da mukamin Mataimakin Darakta-Janar mai kula da tuntuba da wayar da kan jama’a a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na ADC, ya yi haka ne a wurinngangamin kamfe da aka gudanar a Jihar Kebbi.

Kara karanta wannan
Nafiu Bala ya fito yana murna da rusa takarar Atiku da dukkan 'yan ADC a Najeriya

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa an ga Melaye a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta yana jagorantar dandazon magoya bayan jam’iyyar wajen furta kalmar.
Hakan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yanke hukuncin rusa shugabancin ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark da duk wasu ayyuka da tsagin ya yi.
Daga cikin ayyukan tsagin David Mark da hukuncin kotun ya shafa har da tsaida tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Dino Melaye ya fallasa kudin SWV
Da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar a gangamin, tsohon sanatan ya kwatanta kudaden da ake zargin an kashe a karkashin tsarin Service-Wide Votes (SWV) a lokacin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da na gwamnatin Tinubu.
Melaye ya ce:
“A lokacin gwamnatin Buhari, ya kashe Naira tiriliyan shida kacal a kan Service-Wide Votes cikin shekaru takwas, amma Tinubu ya kashe Naira tiriliyan 26 cikin shekaru uku kacal. Shin wannan bai isa mu rika rera Ole Ole Ole, ma'ana ‘Barawo, Barawo, Barawo’ ba?”
Wannan furuci ya sa dandazon magoya bayan jam’iyyar suka shiga rerawa tare da shi.
Daga bisani, Melaye ya bukaci jama’ar da ke wurin su yi wa Tinubu “Allah Ya Isa” sau uku, inda magoya bayan suka maimaita kalmar.
Daga nan sai ya bukace su da su kara masa gyara guda daya, yana cewa: “Ku kara masa daya.”

Source: Facebook
Ma’anar Allah Ya Isa
“Allah Ya Isa” wata kalma ce ta Hausa da mutane kan yi amfani da ita wajen neman taimakon Allah ko hukuncinsa idan suka ji an zalunce su, an cuce su ko an danne su.
Kalmar tana nuna mika lamari ga Allah a matsayin babban mai hukunci, musamman idan mutum ya ga cewa hanyoyin neman adalci ta hannun mutane ba su wadatar ba.
Ana ganin APC na tsoron Atiku
Kun ji cewa tsohon gwamnan Edo, Oserheimen Osunbor ya ce alamu sun nuna APC na tsoron fuskantar ɗan takara mai ƙarfi kamar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Mai ba da shawarar kan harkokin shari’a na ADC ya ce jam’iyyar da ɗan takararta na shugaban ƙasa za su ci gaba da yaƙin neman zaɓensu saboda sun yi imanin cewa hukuncin kotun da ya soke takarar Atiku ba zai tabbata ba.
Asali: Legit.ng
