Abba Hikima ya yi magana game da shigar ‘yan gwagarmayar Najeriya cikin siyasa

Abba Hikima ya yi magana game da shigar ‘yan gwagarmayar Najeriya cikin siyasa

  • Abba Hikima bai da matsala idan masu gwagwarmaya da rajin kare al’umma sun tsunduma cikin harkokin siyasa
  • Amma lauyan bai ganin dacewar takwarorinsa su shiga jam’iyyar APC da suka dauki lokacin suna sukar gwamnatinta
  • Hikimay ana da ra’ayin cewa ‘yan gwagarmaya su kafa tasu jam’iyyar ko kuma su yi adawa har su samu shugabanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Abba Hikima Fagge Esq. ya shiga maganar da ake ta yi dangane da shigar ‘yan gwagwarmaya cikin harkokin siyasa a damu da su.

Fitaccen ‘dan gwagwarmayar ya ga bukatar hakan ne ganin an taso wasu daga cikin tsofaffin abokan tafiyarsu a gaba da zargin sun shiga APC.

Abba Hikima
Abba Hikima da wasu 'Yan Tinubu Must Go a wajen Atiku Abubakar Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

Abba Hikima bai adawa da shigar 'yan gwagwarmaya siyasa

A shafin Facebook, Abba Hikima yake cewa babu laifi idan abokansa na gwagwarmaya sun shiga siyasa, asali ma su suka fi dacewa da mulki.

Kara karanta wannan

"Dan takarar haɗakar adawa zai iya kayar da Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027"

Sai dai duk da haka, ya nuna adawarsa da shiga jam’iyyar APC mai mulki wanda suka yi shekara da shekaru suna tir da salon gwamnatocinsu.

Hikima Fagge ya zargi APC da ginuwa a kan zalunci saboda haka ya ce ba daidai ba ne kuma ‘yan gwagwarmaya su bi sahun jam’iyyar.

Lauyan bai yi na'am da shiga APC ba

Masanin shari'ar ya rubuta:

“Babu wanda yake cewa 'yan gwagwarmaya ba su da damar shiga siyasa. A haƙiƙa ma, 'yan gwagwarmaya su suka fi kowa dacewa su shiga siyasa domin su suka fahimci damuwar jama'a da halin da al'umma take ciki.

Kara karanta wannan

'Za ku dawo sayen fetur a N200 idan kuka zabe ni,' Dan takarar SDP

Abin da muke cewa shi ne, bai kamata 'yan gwagwarmaya su shiga cikin jam'iyya mai mulki da suka shafe tsawon lokaci suna zargi ba. Jam’iyyar da ta ginu akan zalunci ba, domin hakan zai zama tamkar yaudarar al'umma.

Lauyan ya ce irin haka ta sa a baya ya ankarar da jama’a cewa ‘yan tafiyar matasa sun soma shinshinar APC don babu bukatar a boye wa kowa.

Hikima yake cewa idan mai rajin kare hakkin al’umma ya kutsa kai cikin irinsu APC, babu wani sauyi na a zo-a gani da zai iya kawo wa a Najeriya.

Tarihin 'yan gwagwarmayar da suka shiga APC

Ya kawo misali da wasu ‘yan gwagwarmayar da suka rabu da kare jama'a, suka yi nutso a siyasa, a tunanin shi babu wani abin kirki da suka canza.

Daga cikinsu har da tsohon shugaban kungiyar kwadago, fitattun ‘yan gwagwarmaya da wadanda suka yaki mulkin soja a lokacin Janar Sani Abacha.

Abba Hikima ya ce:

"Mun ga misalai na mutane da dama da suka yi gwagwarmaya a baya amma suka gaza yin wani katabus na sauya tsarin bayan sun shiga cikin gwamnati ko jam'iyya mai mulki wadda tayi ƙaurin suna a zalunci, misali: Adams Oshiomhole, Festus Keyamo, Dr. Aminu Gamawa, Shehu Sani, Uba Sani, da Bayo Onanuga duk yan gwagwarmaya ne.

Kara karanta wannan

Fashola ya yi bayani kan zargin amfani da EFCC wajen tilasta wa gwamnoni komawa APC

Amma me suka fi sauran yan siyasa a yanzu? Me suka canja?

Shawarar da Hikima ya ba masu gwagwarmaya

Shiyasa ya kawo shawarar su kafa jam’iyyar su ta dabam kamar yadda wasu takwarorinsu suka yi a ksashen duniya lokacin da suke neman mulki.

Hakan ta faru da Nelson Mandela, Thomas Sankara, Ousmane Sonko, Bassirou Diomaye Faye, Gabriel Boric, Lula da Silva, da Václav Havel a Czech.

Ya kawo shawarar cewa idan sun gaza hakan, su shiga jam'iyyar adawa mai kwari su kifar da APC, ya ce akasin hakan zai jawo masu fushin jama’a.

Ana yi wa jagoran TinubuMustGo barazana

An ji cewa matashin ɗan gwagwarmaya Abdul Turaki ya ce ana yi masa barazanar kisa bayan ya zargi Dan Bello da yin aiki a asirce da Seyi Tinubu.

Barazanar ta biyo bayan ikirarin da ya yi cewa gwamnati na ƙoƙarin sayen masu fafutukar "Tinubu Must Go".

Kungiyar Amnesty International ta bukaci jami'an tsaro da su gaggauta binciken lamarin domin kare lafiyar Abdul Turaki wanda yake adawa da APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng