Kwankwaso Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa bayan Zargin Abba da Shuna Shi ga EFCC

Kwankwaso Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa bayan Zargin Abba da Shuna Shi ga EFCC

  • Wani mai fafutukar tabbatar da gaskiya ya musanta zargin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kitsa shigar da Sanata Kwankwaso kara gaban EFCC
  • Bashir ya ce babu wata alaka tsakanin gwamnan Kano da kungiyar SACGGI, yana mai cewa Kwankwaso bai gabatar da hujjar da ke tabbatar da zarginsa ba
  • Ya bukaci Kwankwaso ya mayar da hankali kan amsa zarge-zargen da ake yi masa maimakon dora alhakin lamarin kan gwamnan Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani mai fafutukar tabbatar da gaskiya, Imam Musa Bashir, ya yi watsi da zargin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin Kano.

Ana zargin Abba Kabir Yusuf ya kitsa shigar da shi kara gaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da kungiyar Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative (SACGGI).

Kara karanta wannan

Gobara ta yi gagarumar ɓarna a kasuwar Kano, Gwamna Abba ya ba da tallafin Naira miliyan 100

An soki Kwankwaso bayan zargin Abba Kabir
Gwamna Abba Kabir da Rabi'u Musa Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Da yake magana a Abuja, Bashir, ya bayyana zargin a matsayin karya da abin kunya, yana mai cewa Kwankwaso bai gabatar da wata hujja da ke alakanta gwamnan da kungiyar ba, cewar Leadership.

An kare Abba Kabir kan zargin Kwankwaso

Bashir ya ce Gwamna Abba ba shi da wata alaka da kungiyar SACGGI, domin bai kafa ta ba, bai dauki nauyin ayyukanta ba, kuma bai ba ta izinin shigar da kara ko gudanar da zanga-zanga a madadinsa ba.

Ya kara da musanta cewa Abba Kabir Yusuf ya nemi EFCC ta bi diddigin Kwankwaso ko kuma ya yi amfani da kafafen yada labarai, mambobin majalisarsa ko hukumomin gwamnati wajen bata sunan tsohon gwamnan.

Bashir ya bayyana cewa alakar Kwankwaso da EFCC ta samo asali ne tun kafin Abba Yusuf ya zama gwamnan Kano.

Ya ce:

"Shari'ar Kwankwaso da EFCC ta riga ta fara kafin Gwamna Abba ya hau mulki, saboda haka bai kamata a dora masa alhakin hakan ba."

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina ya tsoma Ganduje da Abba ke 'karar' Kwankwaso ga EFCC

An kare Abba Kabir kan zargin Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

An soki Kwankwaso kan zargin Abba Kabir

Mai fafutukar ya bayyana zarge-zargen a matsayin dabarar siyasa da aka kulla domin juya ra'ayin al'umma kan gwamnan Kano gabanin zaben 2027.

Ya shawarci Kwankwaso da ya mayar da hankali wajen kare kansa kan zarge-zargen da ake yi masa maimakon zargin Gwamna Abba da hannu a lamarin.

Dangane da dan takarar NDC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Bashir ya ce Gwamna Yusuf ba shi da ikon juya shawarar hukumar zabe ko kotuna, don haka ya kamata duk wanda ke da korafi kan takarar ya kai shi gaban jam'iyyar.

Ya ce:

"Gwamnan ba ya bukatar hana kowa tsayawa takara. A bar kowa ya fito takara, al'umma ce za ta yanke hukunci."

Bashir ya kara da cewa Gwamna Yusuf a shirye yake ya tsaya takara, kuma yana da yakinin samun nasara a karkashin jam'iyyar APC.

Ya ce gwamnan ya mayar da hankali wajen bunkasa Kano ta hanyar biyan albashi da fansho, inganta ilimi da kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa da kuma kyautata walwalar jama'a.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Mutumin Kwankwaso, Dantiye ya fadi wanda zai zaba a Kano

EFCC: Kwamishinan Ganduje ya soki Abba Kabir

Kun ba ku labarin cewa tsohon kwamishinan Kano ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da nuna rashin adalci kan kai karar Rabiu Kwankwaso ga EFCC.

Mu’azu Magaji ya ce bai kare Kwankwaso daga duk wani zargin rashawa ba ne, sai dai yana tambayar dalilin da ya sa gwamnati ke mayar da hankali kansa.

Gwamnatin Kano ta musanta hannu a binciken Kwankwaso, tana mai cewa alakarsa da hukumar ta fara ne tun kafin gwamnatin Abba Yusuf ta hau mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.