'Yan Najeriya Sun Raɗawa Atiku Sabon Suna gabanin Zaben Shugaban Kasa na 2027

'Yan Najeriya Sun Raɗawa Atiku Sabon Suna gabanin Zaben Shugaban Kasa na 2027

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya amince da sunan “Daddy Subsidy” da magoya bayansa suka rada masa
  • Atiku wanda ke neman takarar shugaban kasa, ya ce sauƙi na tafe wa ’yan Najeriya, inda ya yi alƙawarin dawo da sauƙin rayuwa a ƙasar
  • Jam’iyyar ADC ta taya tsohon mataimakin shugaban ƙasar murnar cika shekara 80 da haihuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya amince da sunn “Daddy Subsidy” da magoya bayansa suka fara kiransa da shi.

Yan Najeriya sun fara kiran Atiku da wannan lakabi ne sakamakon alkawarin da ya yi na dawo da tallafim fetur idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2027.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku ya karbi sunan Daddy Subsidy

Kara karanta wannan

Bayan kamfe ya kankama, an sake neman Atiku ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027

Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, yayin da yake godiya ga waɗanda suka taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Ya ce sauƙi na tafe wa ’yan Najeriya, tare da yin alƙawarin dawo da yanayin da rayuwa za ta kasance mai sauƙi a ƙasar.

A cikin saƙon nasa, Atiku ya rubuta cewa:

“Daga cikin sunayen da ’yan Najeriya suka rada mini, ‘Daddy Subsidy’ ne wataƙila sunan da na fi jin daɗinsa a ranar haihuwata. Na gode da kyawawan saƙonninku da addu’ar da ta faranta mini rai a wannan rana.
“Ga ’ya’yana maza da mata da suka bazu a sassan ƙasar nan: sauƙi na tafe, kuma zai biyo baya, zan sake mayar da Najeriya ƙasa mai sauƙin rayuwa.”

Yadda sabon sunan ya samo asali

Atiku ya yi wannan martani ne ga saƙon taya shi murnar ranar haihuwa da wani mai suna Folarin Sode, wanda ke amfani da shafin @flosode a dandalin X, ya wallafa.

Sode ya rubuta cewa:

“Barka da ranar haihuwa, Daddy Subsidy. Ina yi maka fatan alheri, Alhaji Atiku Abubakar GCON, uban Najeriya mai nagarta. Mu ’ya’yanka a sassan ƙasar nan muna ɗokin dawowarka domin ka kawo mana ɗauki. Allah Ya ba ka alheri a yau da kuma kowace rana.”

Kara karanta wannan

Atiku ya taso Tinubu da NNPCL gaba a yi bayanin inda Naira tiriliyan 1.4 ya maƙale

Atiku ya cika shekara 80 da haihuwa ne ranar Talata. Ya daɗe yana kira da a dawo da tallafin man fetur da aka tace a cikin gida, amma a mayar da shi ga waɗanda suka cancanta, domin rage kuɗin sufuri da na samar da kayayyaki.

An nemi Atiku ya janye takararsa ta 2027

A wani labarin, kun ji cewa Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Bode George, ya bukaci Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027.

George ya ce bisa tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, ana sa ran kujerar shugaban ƙasa za ta koma Arewa a shekarar 2031, don haka Atiku zai iya sake neman takarar a lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262