2027: Abin da Sheikh Jalo Jalingo Ya Fada wa Mabiyansa dangane da Wanda Za a Zaba
- Ibrahim Jalo Jalingo bai goyon bayan a zabi wata jam’iyyar da ba APC ba a takarar shekarar 2027 a jihar Taraba
- Babban malamin na kungiyar Izala ya cigaba da tallar tikitin Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima
- Sheikh Jalo Jalingo yana ganinAPC ce maslaha bayan shekara da shekaru ana gallaza masu a siyasar Taraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Taraba - Ibrahim Jalo Jalingo ya cigaba da aikin da ya dauko na tallar gwamnatin Musulmi da Musulmi a jiharsa ta Taraba.
Wannan karo Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo bai tsaya a iyaka Bola Ahmed Tinubu, ya nuna a yi APC daga sama har kasa.

Source: Facebook
Shawarar da Ibrahim Jalo Jalingo ya bada
A wani rubutu da yake shafin Facebook na malamin addinin, ya ba wadanda suka isa da shi shawarar su zabi jam’iyyar APC.
Jalo Jalingo ya ce sun fi shekaru 20 suna shan wahala a jihar Taraba, ya kuma ce goyon bayan APC ita ce mafita a zaben 2027.
SHAWARAR DA MUKA BA WA AL'UMMARMU TA TARABA:
1. Mun ba wa al'ummarmu ta jihar Taraba masu daraja shawarar cewa su nuna haƙuri da hankalta su zaɓi jam'iyyar APC; domin ta hakan ne in sha Allah za mu hau turbar kuɓuta daga tahmiicin da muke cikinsa a Jihar tun fiye da shekaru 20.
Malamin Musuluncin ya nuna cewa daga 2006 har yau ba a dama wa da su a jihar ta Arewa maso gabas.
Sheikh Jalingo ya bada shawarar cewa kada kuri’a da jam’iyyun adawa na APGA ko PDP yana nufin zalunci ya cigaba a Taraba.
Mun ce da su: Zaɓen PDP da APGA tamkar neman zaluncin da aka dasa mana ne tun daga 2006 ya ci gaba da wanzuwa har abada.
Jalo Jalingo bai tare da takarar Atiku Abubakar
Goyon bayan jam’iyyun ADC da NDC a zabe mai zuwa kuwa tamkar Musulman Taraba su koma gidan jiya ne a siyasa.
Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi suke rike da tikitin ADC, sai kuma Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su ne ke takara a NDC.
A game da ADC da NDC da ke neman raba jam’iyyar APC da mulki, sai ya ce:
3. Mun ce da su: Zaɓen ADC da NDC kuwa tamkar ƙoƙarin maimaita abin da muka yi ta yi ne fiye da shekaru 20 da suka wuce, ko da yake dai muna tsammanin samun lada a kan hakan toh amma hakan bai kai mu ga natijar da muke son kaiwa gare ta ba.
Ya kare shawarar shi da yin kira a bi bayan jam’iyyar APC mai rike da mulki.
4. Lalle abin da ya fi dacewa a zaɓen bana shi ne dukkan al'ummarmu su ƙara haƙuri su zaɓi jam'iyyar APC. Allah Maɗaukakin Sarki muke roƙon Ya taimake mu. Ameen.
- Jalo Jalingo
Gwamnan jihar, Kefas Agbu ya ci zabensa ne a PDP a 2023 amma daga baya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin kasa.
Sakon bai yi nuni da cewa malamin yana kira a zabi Bola Tinubu ne kawai ko kuma har da sauran ‘yan takaran jam'iyyarsa a Taraba ba.
Bola Tinubu ya shirya liyafa a Makkah
A wata liyafa da shugaban Najeriya ya kira a Saudi, an ji labari ya ci abinci da gwamnoni da manyan gwamnati a kasa mai tsarki.
An ga Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnoni irinsu Uba Sani, Babangana Zulum da Umar Namadi suna cin abinci jiya a birnin Makkah.
Sauran wadanda aka yi liyafar da su sun hada da hadiman shugaban kasa a fannonin tsaro da siyasa da kuma wasu manyan attajirai.
Asali: Legit.ng


