An Yi wa Shehin Malamin Musulunci Rashin Kunya a Masallaci kan Tinubu
- Wani rikici ya barke a wani masallaci a Taraba bayan wani mai ibada ya kalubalanci Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo kan gwamnatin Tinubu
- Sheikh Jalo Jalingo ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba ta zaluntar jama'a, amma wani mai sallah ya fito ya ce karya yake yi
- Malamin ya bukaci al'ummar Taraba su yi hakuri, su zabi APC a 2027, inda wasu masu amfani da Facebook suka soki matsayinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jalingo, Taraba - An samu hayaniya a masallaci a Taraba bayan wani mai ibada ya kalubalanci Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo kan gwamnatin Bola Tinubu
Wani wa'azin Juma'a da malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo, ya gabatar a jihar Taraba ya haddasa rashin jituwa bayan wani mai ibada ya kalubalanci matsayinsa kan gwamnatin Bola Tinubu.

Source: Facebook
Lamarin ya faru ne yayin sallar Juma'a a wani masallaci, inda malamin yake gabatar da hudubarsa ga al'ummar Musulmi a wani bidiyo da Arewa One TV ta wallafa a Facebook.
Tinubu: An yi hayaniya a masallacin Juma'a
Rahotanni sun bayyana cewa Jalo Jalingo yana magana ne kan gwamnatin Tinubu, lokacin da ya bayyana cewa gwamnatin ba ta zaluntar jama'a.
Sai dai wani mai ibada ya kalubalanci wannan furuci nan take, inda ya yi ihu yana cewa:
"Wannan karya ne!"
Wani faifan bidiyo da aka dauka a cikin masallacin ya nuna wasu daga cikin masu ibada suna fita daga masallacin domin nuna rashin amincewarsu yayin da takaddamar ke gudana.
Lamarin ya ja hankalin jama'a a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka bayyana ra'ayoyinsu kan kalaman malamin da martanin wasu daga cikin masu ibadar.
A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar Asabar, Jalo Jalingo ya ba al'ummar jihar Taraba shawara, inda ya bukace su da su yi hakuri tare da zaben jam'iyyar APC mai mulki a zabuka masu zuwa.
Ya rubuta cewa:
"Mun shawarci al'ummar jihar Taraba da muke girmamawa da su yi hakuri, amfani da hikima da kuma nuna dattaku a siyasa ta hanyar zaben jam'iyyar APC.
Ta wannan zabin, In Sha Allah, muna ganin za mu iya sanya kanmu a hanyar samun 'yanci daga zalunci da rashin adalcin da jiharmu ta sha tsawon shekaru sama da 20."
Malamin ya kara da cewa zaben jam'iyyar PDP da All Progressives Grand Alliance (APGA) zai zama kamar ci gaba da goyon bayan abin da ya bayyana a matsayin rashin adalci da aka dade ana yi a jihar.

Source: Facebook
Martanin masu amfani da Facebook
Sakon malamin a Facebook ya haifar da martani mabambanta, inda masu sharhi da dama suka fara tambayar matsayinsa da kuma kiransa ga mazauna jihar da su goyi bayan APC.
Rufai Abubakar Fta ya tambayi ko matsayar malamin ta siyasa tana da nasaba da muradun al'umma ne ko kuma bukatun kansa.
Ya rubuta cewa: "Wannan burinka ne da kuma neman amfanin kanka, ba wai don al'ummar jihar Taraba ko 'yan Najeriya ba."
Wani mai sharhi, Malam Adamu Chilariye, ya zargi malamin da barin sha'awar siyasa ta shafi yadda mutane suke amincewa da koyarwarsa ta addini.
Ya rubuta cewa:
"Ka sanya mutane sun daina sauraron abin da Allah da Manzonsa suka fada saboda shiga harkokin siyasa da neman amfanin kanka."
Yan bindiga: An ceto wasu malaman Musulunci
Mun ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da ceto limaman Musulunci uku daga cikin shida da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Muhammad Bello, ya ce an ceto limaman ne ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban, ciki har da DSS.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da samame domin gano sauran limaman uku da ke hannun masu garkuwa da mutane tare da kubutar da su.
Asali: Legit.ng


